IQNA

Ahamadinejad Zai Halarci Taron Debe Kewa Da Kur'ani Mai Tsarki

9:18 - August 13, 2011
Lambar Labari: 2169450
Bangaren kur'ani, shugaban kasar Iran Mahmud hamadinejad zai halarci wani zaman taron debe kewa da kur'ani mai tsarki da za a gudanar a birnin Tehran tare da halartar makaranta da mahardata kur'ani a yau 22 ga Mordad.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, rahoton da ya samu daga cibiyar shirya tarukan kur'ani mai tsarki ya yi nuni da cewa, shugaban kasar Iran Mahmud hamadinejad zai halarci wani zaman taron debe kewa da kur'ani mai tsarki da za a gudanar a birnin Tehran tare da halartar makaranta da mahardata kur'ani a yau, da kuma wasu daga cikin jami'ai kamar dai yadda rahoton ya tabbatar.

Wani rahoton kuma na daban ya bayyana cewar wata tawagar manyan jami'an kasar Iran a karkashin jagorancin shugaban kwamitin tsaro da siyasar harkokin waje na Majasilar shawarar musulunci ta kasar Ala'eddin Boroujerdi ta kai ziyara a kasar Masar inda kuma ta gana da manyan jami'an kasar.
Ita dai wannan tawaga wacce ita ce mafi girma daga nan Iran da ta ziyarci kasar ta Masar tun bayan faduwar Husni Mubarak daga kan karagar mulki, ta mika goron gayyata ga kasar ta Masar domin ta halarci wani taron nuna goyon baya ga gwagwarmayar Intifada ta al'ummar Palasdinu wanda za 'a gudanar a farkon watan oktoba mai zuwa a nan birnin Tehran.
Tun daga lokacin da aka kori Mubarak daga kan karagar mulkin kasar ta Masar ne dai ake kara samun kusanci tsakanin kasashen biyu, abin da shugaban Kungiyar 'Yan'uwantaka tsakani Iran da kuma Masar mai suna Ahmed Al-gham-rawy ke cewa babban abin farin ciki ne ga al'ummomin kasashen biyu.

841603
captcha