Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, wuraren da ake gudanar da karatun kur'ani mai tsarki suna daga cikin wurare na lambunan aljanna amma cikin gidan duniya kamar yadda wani daya daga cikin fitattun malmai mai jagorancin sallar juma'a a birnin Thran ya sheda.
Ayatollah Sayyid Khatami ya bayyana hakan ne a lokacin yake gabatar da wani jawabi a gaban rundunar jami'an tsaro, wasu daga cikin ahlul kitab a lokacin ma'aki duk da masaniyar da suke da ita ta zuwan kur'ani mai tsarki daga Allah madaukin sarkin bayan littafan Attauara da Injinla, amma ba a shirye suke ba su yi imani da manzon karshe, kuma su karbi kur'ani mai tsarki a matsayin littafin da ya zo daga Allah madaukakin sarki.
Wannan aya ta ba su amsa da cewa, a tsawon tarihi Allah yana aiko annabawa domin shiryar da mutane, wasu daga cikinsu ana ba su sha'ri'a da littafi, dukaknin wadannan annabawa sun gasgata junasu, saboda dukakninsu daga Allah ubagiji daya suke, kuma sakonsa ne suke isarwa ga 'yan adam. A kan haka babu wani abun mamaki, domin kuwa ubangijin da ya safkar da Attauara ga annabi ya safkar da Injila ga annabi Isa (AS), shi ne ya safkar da kur'ani ga manzon Muhammad (SAW).
842707