IQNA

Bayar Da Amsoshi Dangane Da Ilmomin Tajwidi A baje kolin Kur'ani

17:14 - August 23, 2011
Lambar Labari: 2175717
Bangaren kur'ani, an fara gudanar da wani shiri na bayar da amsoshi ga masu tambaya a wurin taron baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya da ake gudanarwa abirnin Tehran, wanda malam Sabz Ali ke amsawa.



Kamfanin dilalncin labaran iqn adaga wurin taron baje kolin kur'ani ya habarta cewa, an fara gudanar da wani shiri na bayar da amsoshi ga masu tambaya a wurin taron baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya da ake gudanarwa abirnin Tehran wanda malam Sabz Ali ke amsawa tare da halartar wasu daga cikin malaman jami'a a wurin.

Kamar yadda ya zo a cikin ayar da ta gabata, duk wanda ya nemi yardar Allah a cikin aikinsa, wani adadi na makiya Allah ba zai tsorata shi, koda kuwa yana cikin wani mawuyacin hali, kamar yadda muka ambata dangane da musulmi da suka samu raunuka a yakin Uhud, amma wannan ayar mai albarka tana yin Magana ne ga masu raunin imani.

Inda take jan hankalinsu da kada su ba shaidan kafa a cikin zukatansu, har ya samu damar kautar daga tafarkin Allah, idan mutum ya kama wata hanya da ba ta ubangiji ba, to hakika shaidan zai samu wurin zama a cikin zuciyarsa, zai hadu da kaskanci a cikin lamurransa, alhali ko daukaka tana ga Allah da manzonsa da kuma muminai.

Alkur'ani mai tsarki yana magana da musulmi yana cewa; idan kun kasance masu gaskiya a cikin imaninku, to kada ku karkata ga abin da shedan ke raya ma abokansa na daga tsoro, ku ji tsoron Allah shi kadai, kada ku bari karfin makiya ko yawansu ya tsorata ku ya firgita ku, domin kuwa duk yawansu da karfinsu ba su kai karfin Allah madaukakin sarki ba, kuma shi ne mai iko a kan komai.
847908
captcha