Bangaren kur'ani, ratar da Allah yake baiwa masu saba masa ba gazawa ba ce, Allah yanayin hakan ne saboda dalilai guda biyu. Na daya: saboda ya ba su lokaci ko wata kila daga baya su hankalta su dawo ya tuba su koma zuwa ga Allah. Na biyu: Idan har mutum ya bar gidan duniya a kana bin da yake yi ba tare da ya tuba, to Allah zai kama shi da hujja.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da bayanin malman tafsiri suke sun bayyana cewa, Tsawon rayuwa ba shi ne muhimmi ba, yin amfani da ita wajen biyayya ga Allah shi ne muhimmi. Imam Sajjad (AS) yana rokon Allah da cewa; idan rayuwarsa za ta zama abin wasa a hannun shaidan, to Allah ya taikaita rayuwarsa a kan imani da biyayya gare shi.
Kwamitin kula da harkokin musulmi na yankin Jamu a Keshmir da ke karkashin ikon kasar India ya bayyana cewa hakika hukumar da Imam Ali (AS) ya kafa babbar abin koyi ce ga dukaknin mutanen duniya kamar dai yadda dukaknin malman tarihi suka tabbatar, kuma aka gani rubuce a cikin littafai da dama na addini.
Kada a yanke hukunci kai tsaye da ayyukan kafirai da azzalumai, karshensu shi ne abin yanke hukunci da shi, haka nan kuma kafircin wadannan mushrikai ba zai cutar da Allah madaukakin sarki da komai ba. Maimakon haka ma su ne suke cutuwa da kafirci da shirkarsu, kuma su koma zuwa ga Allah su shiga azaba mai radadi.
846060