Kamfanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin al'alam an bayyana cewa, limamin masalacin garin Saida kuma daya daga cikin fitattun manyan malaman addini a kasar Lebanon ya bayyana ranar qods a matsayin ranar yin fada da girman kan manyan kasashen duniya baki daya ba kawai yahudawan sahyuniya ba bisa la'akari da cewa dukaknin ayyukan zalunci da suke yi hakan na kasancewa ne karkashin goyon bayan da suke samu daga irin wadannan kasashe.
Malamin ya ci gaba da cewa wannan rana tana alamta cikakken goyon baya ne ga dukaknin al'ummomi da ake zalunta aduniya baki daya, kuma hakan zai sanya a cikin ransu cewa lallai ashe akawi ruhin taimakon raunana a duniya, maimakon yanke kauna daga duk wani yunkurin 'yantar da wadanda ake bautarwa.
Hakan na daga cikin muhimamn abubuwa da wannan juyin juya hali ya gadawar al'ummar musulmi, musamman ma wadanda ake zalunta daga cikinsu, kuma amfanin hakan zai koma ne ga dukkanin al'ummomi, musulmi da wadanda ba musulmi bad a suke fuskatar zalunci daga kasashen duniya masu girman kai da kuma munafukai daga cikin shugabannin larabawa da na musulmi.
Sheikh Mahir Hammud daya daga cikin fitattun manyan malaman addini a kasar Lebanon ya bayyana ranar qods a matsayin ranar yin fada da girman kan manyan kasashen duniya baki daya ba kawai yahudawan sahyuniya bad a suke zaluntar al'ummar palastinu da sauran musulmi. 849034