Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa cewa, Ali Al-adib, daya daga cikin jagororin jam’iayar da’awa a Iraki ya bayyana cewa malaman akidar wahabiyanci an kasar Saudiyya suna fitar da fatawoyi na halasta jinin al’ummar kasar Iraki mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah lamarin da ke jawo hare-haren ta’addancin da ake kaiwa a kasar da suna jihadi kan kafirai.
Sau da yawa kur’ani mai tsarki a wuraren da yake hana mutum aikata wani aiki, ya kan gabatar da halastattun hanyoyi, daga bisani kuma ya nuna ma mutum abubuwann da aka hana masa aikatawa ko haramta ma ci ko sha ko abin da ya yi kama da haka.
Ayar da ta gabaci wannan ta yi nuni da halascin ababen ci halastattu tsarkaka, inda take nuni da cewa komai halastacce ne gare ku , sai abin da yake cutar da jiki da ruhi, shi ne ya haramta.
An haramta jini da mushe da naman alade saboda cutarsu ta zahiri, amma haramcin dabbobin da mushrikai suke yankawa suna gumaka ba da sunan Allah ba, hakan haramci ne saboda cuta ta badini.
Addinin musulunci addini ne mai sauki da ya fayyace komai ga mutum ga mutum, ta yadda hatta abin da zai cutar da mutum ta fuskacin lafiyarsa yakan yi hani a kansa, kamar yadda yake yin umurni da kyawan dabi’u da kyautatawa da sada zumunci da sauran abubuwa masu kyau ga rayuwar dan adam.
851086