IQNA

Manufar Masu Fasaha Musulmi Ita Ce Isar Da Sakon Addini Ta Wannan Hanya

20:09 - August 29, 2011
Lambar Labari: 2178928
Bangaren kasa da kasa, masu fasaha daga cikin musulmi suna yin amfani da wannan baiwa da Allah ya ba su domin su isar da sakon addini ga sauran mutane da suke duba ayyuakan fasahar da suke gudanarwa.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo Musulunci addini ne da ya dora ka'idoji da suka dace da dabi'a ta dan adam, a matsayi na daidaiku da kuma a mataki nazamantakewarsa, irin wadannan ka'idoji sun hada da shari'a da hukunce-hukuncen da suke cikinta, ta yadda bin irin wanan sahihin tsari na addini muslunci shi ne kubutar mutum da kuma al'ummarsa, ta fuskar tsaronsa, rayuwarsa ta duniya da lahira, da ma samun natsuwar zuci, ta yadda rashin bin dokokin Allah kan sanya mutane su shiga fagamniyya da rashin natsuwa, ta jiki da ta ruhi.
Misali, yin kisan kai a cikin al'umma, idan mutun ya san cewa ga hukuncin da zai hau kansa idan ya kashe mutum daidai da shari'a ta addinin muslunci, zai yi shayin yin hakan ko da ba don tsoron Allah ba, domin tunain abin da zai je ya dawo kan rayuwarsa.
To lokacin da mutane suke jin haka, za a samu karancin kasashe-kashe a cikin al'umma, kenan ta nan musulunci ya tababbatar da tsaro ta hanyar shari'arsa da tsarinasa a cikin rayuwar jama'a ta zamnatakewa.
850585




captcha