Bangaren kasa da kasa, gungun 14 ga watan Fabrairu na na kasar Bahrain ya kirayi dukkanin al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin shiga cikin zanga-zangar fayyace makoma karo na 8 a kasar ta Bahrain.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam an bayyana cewa, kwamitin 14 ga watan Fabrairu na na kasar Bahrain ya kirayi dukkanin al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin shiga cikin zanga-zangar fayyace makoma karo na 8 da za a gudanar a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gungu ya yi wannan kira ne domin gudanar da gangamin a ranar alhamis zuwa a dukkanin garuruwan kasara ranar alhamis 17 ga shahrivar karfe 19:30, wanda kuma ga dukkanin alamu mutane a shirye suke su karba wannan kira domin ci gaba da nuna rashin goyon bayan zaluncin masarautar kasar.
Babbar manufar masu wannan zanga-zanga dai ita ce neman a yi sauye-sauye a cikin harkokin mulki da siyasa akasar ta Bahrain, amma sarakunan kasar da suke samun cikakken goyon baya daga masarautar Saudiyya suna ci gaba da yin kunnen shegu da wadannan kiraye-kiraye.
854784