IQNA

18:14 - September 05, 2011
Lambar Labari: 2181910
Bangaren siyasa da zamantakewa, wakilan ofisoshin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran sun jaddada wilaya a hubbaren marigayi Imam Khomeini (RA) tare da mika kyautar wani fankacecen fure a kan kabarinsa.Kamfanin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa wakilan ofisoshin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran sun jaddada wilaya a hubbaren marigayi Imam Khomeini (RA) tare da mika kyautar wani fankacecen fure a kan kabarinsa da ke cikin babbar makabarta.

Dukkanin ma'aikatan dai suna aiki ne a ofisoshin jakadancin jamhuriyar muslunci ta Iran da ke kasashen ketare, wanda ziyarar ta su ta zo a ranar 12 ga watan Shahrivar, wanda hakan ya yi daidai da ranar jaddada alkawali na kare manufofin juyin juya halin muslunci.

Bayanin ya ci gaba da cewa baya ga dora fankacecen fure kan hubbaren, an karanta addu'oi ga ruhinsa da neman gafara gare shi, da kuma rokon Allah ya saka masa da alkhairi kan anmijin kokarin da ya yi wajen tunatar da al'ummar musulmi hanya fita daga karkashin zakuncin makiya Allah.

854039


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: