IQNA

Rahoton Palmer Ya Halasta Ta'addancin Isra'ila Kan Al'ummar Gaza

13:29 - September 06, 2011
Lambar Labari: 2182415
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil adama ta palastinu ta yi kakkausar suka dangane da rahoton da shugaban kwamitin bincike na majalisar dinikin duniya ya fitar kan ta'addancin Isra'ila a yankin Gaza.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa kungiyar kare hakkin bil adama ta palastinu ta yi kakkausar suka dangane da rahoton da shugaban kwamitin bincike na majalisar dinikin duniya ya fitar kan ta'addancin Isra'ila a yankin zirin Gaza inda ya tabababtar da cewa wannan ya yi daidai, kuma hakan bai saba wa shai'a ba.

Wani rahoton kuma yana cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta gargadi fira ministan kasar Turkiyya dangane da aniyarsa na kai ziyara zuwa yankin Zirin Gaza, wanda duniya tabattar da cewa yahudawan sahyuniya sun yi kisan gilla a kan a fararen hula da suke yankin.
Jaridar Jerusalam Post da ake bugawa a haramtacciyar kasar Isra'ila ta bayyana cewar ziyarar da fira ministan kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdugan ke son kai wa yankin Zirin Gaza wani babban kuskure ne a fuskar diflomasiyya kuma lamari ne da zai zame matsala ga kasar.
Jaridar ta Jerusalam Post ta kuma nakalto daga majiyar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila cewa; ziyarar Erdugan zuwa Gaza zai haifar da matsala a alakar da ke tsakanin kasar Turkiyya da Amurka, kuma hukumar cin gashin kan Palasdinawa zata dauki ziyarar a matsayin maras halacci.
854807
captcha