Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habrta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an sheda cewa, Hojjatol Islam Mohammadi Golpaigani ya ce shugaban ofishin jagoran juyin juya halin muslunci na Iran ya bayyana cewa babban aikin da ke kan jakadojin jamhuriyar muslunci a kasashen ketare shi ne fito da matsayin juyin juya hali da kuma marigayi Imam Khomeini Allah ya yi masa rahama.
A bangare guda kuma ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba zata taba sakacin mai da martani kan duk wani harin wuce gona da iri da za a kaddamar kan kasarta ba.
Ministan tsaron kasar Iran Brigadier Janar Ahmad Wahidi ya bayyana cewar shirin kungiyar tsaro ta kasashen turai na neman kafa na'urar kakkabo makamai masu linzami da na hangen nesa a cikin kasar Turkiyya da nufin kalubalantar makamai masu linzami da kasar Iran take mallaka; barazana ce ga tsaron kasar Iran, don haka kungiyar tsaro ta ta kwana cikin shirin fuskantar mai da martani mai tsanani matukar ta yi gigin kaddamar da harin soji kan kasar ta Iran.
Janar Wahidi ya kara da cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana daukan jibge rundunar sojin Amurka da na kasashen yammacin Turai a kasashen musulmi a matsayin wata matsala da ke tada hankali, kuma lamari ne da ke janyo cikas a fuskar tsaro da zaman lafiyan kasashen.
856379