IQNA

Kasashen Duniya Sun Rufe Idanunsu Kan Abin Da Yake Faruwa A Bahrain

20:33 - September 08, 2011
Lambar Labari: 2183695
Bangaren kasa da kasa, wasu dag acikin kasashen duniya sun rufe idanunsu dangane da abin da yake faruwa acikin kasar Bahrain na kisan kiyashin da ake yi wa mutanen kasar a hannun mahukuntan da suke samun goyon bayan Amurka da Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tahsar Al-alam cewa wasu daga a cikin kasashen duniya sun rufe idanunsu dangane da abin da yake faruwa acikin kasar Bahrain na kisan kiyashin da ake yi wa mutanen kasar a hannun mahukuntan da suke samun goyon bayan Amurka da Saudiyya da wasu daga cikin wawayen shugabannin larabawa.
Kamar yadda muka fada a cikin bayanin ayar da ta gabata, manzon Allah ya umurci dukkanin musulmi da suka halarci yakin Uhud da su kara daura damara domin tunkarar rundunar mushrikai da suke nufin afkawa birnin madina, hakan ya sanya hatta wadanda suka ji raunuka ba a bar su a baya ba wajen aiwatar da wannan umurni na manzo, hakan ya jefa tsoro mai tsanani a cikin zukatan kafirai, inda suka ja baya, bayan sun kudiri aniyar yin kisan gilla a kan muslmi a cikin birnin Madina.
Sai wannan ayar ta safka, domin yaba wa musulmi da kuma jaruntar da suka nuna, wannan ayar tana koyar da mu wani babba darasi, shi ne cewa idan musulmi suka san abin da ya rataya kansu kuma suka yi aiki da umurnin Allah, to za su samu taimakon ubangiji a cikin dukkanin halin da suka samu kansu na tsanani.
856543
captcha