IQNA

Natanyaho Ya Yi Matukar Kaduwa Kan Farmakin Misrawa Kan Ofishinsu

14:05 - September 12, 2011
Lambar Labari: 2185852
Bangaren kasa da kasa, Pira ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Natanyaho ya nuna matukar kaduwarsa dangane da yadda wasu dubban matasa suka kai farmaki kan ofishin jakadancin yahudawan sahyuniya da ke birnin Alkahira.


Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na aynar gizo na jaridar Dastur cewa, Pira ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Natanyaho ya nuna matukar kaduwarsa dangane da yadda wasu dubban matasa suka kai farmaki kan ofishin jakadancin yahudawan sahyuniya da ke birnin Alkahira a ranar Jumar da ta gabata.

Bayaninya ci gaba da cewa fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila zata ci gaba da mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da ke tsakaninta da kasar Masar.
A furucin da ya fito daga bakin fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kwana daya bayan harin da jama'ar kasar Masar suka kai kan ofishin jakadancin h.k.Isra'ila da ke birnin Alkahira; Benyamin Netanyahu ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila zata ci gaba da mutunta yaejejeniyar zaman lafiya da ke tsakaninta da kasar .
Domin hakan shi ne masalahar kasashen biyu, kuma gwamnatin h.k.Isra'ila tana ci gaba da tuntubar gwamnatin Masar domin ganin jakadan Isra'ila ya koma kasar ta Masar cikin hanzari, ya kuma jinjinawa gwamnatin Masar kan matakin da ta dauka na 'yanto jami'an tsaron h.k.Isra'ila shida da aka yi garkuwa da su a cikin ofishin jakadancinta da ke kasar ta Masar, kamar yadda ya yaba wa shugaban kasar Amurka Barak Obama.
858634



captcha