IQNA

16:08 - September 12, 2011
Lambar Labari: 2185981
Bangaren kasa da kasa, tattaunawa tsakanin jagororin mabiya addinai na duniya ce kawai za ta bayar da dama gare su fahimci juna ta yadda za su taka gaggarumar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya aduniya a baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo cewa tattaunawa tsakanin jagororin mabiya addinai na duniya ce kawai za ta bayar da dama gare su fahimci juna ta yadda za su taka gaggarumar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya a baki daya ta yadda hakan zai kunyata masu adawa da duk wani shiri na sasantab al’ummomi.
Wasu daga cikin ahlul kitab a lokacin ma'aki duk da masaniyar da suke da ita ta zuwan kur'ani mai tsarki daga Allah madaukin sarkin bayan littafan Attauara da Injinla, amma ba a shirye suke ba su yi imani da manzon karshe, kuma su karbi kur'ani mai tsarki a matsayin littafin da ya zo daga Allah madaukakin sarki.

Wannan aya ta ba su amsa da cewa, a tsawon tarihi Allah yana aiko annabawa domin shiryar da mutane, wasu daga cikinsu ana ba su sha'ri'a da littafi, dukaknin wadannan annabawa sun gasgata junasu, saboda dukakninsu daga Allah ubagiji daya suke, kuma sakonsa ne suke isarwa ga 'yan adam.
A kan haka babu wani abun mamaki, domin kuwa ubangijin da ya safkar da Attauara ga annabi Musa ya safkar da Injila ga annabi Isa shi ne ya safkar da kur'ani ga manzon Muhammad, saboda haka wannan aya ta gaya musu cewa idan da gasket suna neman gaskiya ne, to wajibi ne su yi iani da annabi Muhammad da sakon da ya zo da shi daga Allah.
858743


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: