IQNA

Jam'iyar Musulunci Ta Tunisia Ta Jaddada Wajabcin Yin Zabe Mai Tsabta

11:54 - September 15, 2011
Lambar Labari: 2187648
Bangaren kasa da kasa, jam'iyar masu kishin islama akasar Tunisia ta jaddada wajabcin gudanar da zabuka akasar cikin tsabta wanda kuma rashin yin hakan zai sake jefa kasar cikin wani mawuyacin hali.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na swissinfo an bayyana cewa jam'iyar masu kishin islama akasar Tunisia ta jaddada wajabcin gudanar da zabuka akasar cikin tsabta wanda kuma rashin yin hakan zai sake jefa kasar cikin wani mawuyacin hali bayan wanda ta samu kanta cikin a lokacin mulkin kama karya na Zainul Abidin.

Jagoran kungyar Rashid Ganushi shi ne wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi kan makomar kasar Tunisia, inda ya ce wannan zaben da ake shirin gudanarwa shi ne zabe na farko da za a gudanar zabe sahihi a kasar Tunisia da sauran kasashen larabawa.

Dangane da yadda haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya take ta kokarin ganin ta shiga cikin harkokin kasar, da dama daga cikin jamiyun siyasa sun nuna rashin goyon baya ga duk wani da zai iya baiwa yahudawan sahyuniya shiga cikin harkokin kasarsu.

Babbar jam'iyar masu kishin islama akasar Tunisia ta jaddada wajabcin gudanar da zabuka akasar cikin tsabta wanda kuma rashin yin hakan zai sake jefa kasar cikin wani mawuyacin hali na rikici da rashin sanin makoma takamaimai.

860950



captcha