IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Fadakar Musulmi Tare Da Halartar Ayatollah Khamenei

14:59 - September 17, 2011
Lambar Labari: 2188600
Bangaren siyasa, an fara gudanar da taron fadakar musulmi na farko da ake gudanarwa amataki na kasa da kasa, tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci na Ira Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei.



Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa a yau an fara gudanar da taron fadakar musulmi na farko da ake gudanarwa amataki na kasa da kasa, tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei wanda shi ne ya bude zaman taron, da jawabin da ya gabatar.

Ayatollah Ozma Khamenei a cikin jawabinsa ya mayar da hankali kan muhimman abubuwan da ya kamata wadanda suka yi juyi a cikin kasashen larabawa su kula da su, domin kuwa kasashen yammacin turai sun sha alwashin ganin sun dankwafe yunkurinsu ta kowace fuska da dukkanin hanyoyi.

Bayanin nasa ya ci gaba da cewa, kasashe masu girman kai su ne wadanda suka hada kai da sauran azzaluman shugabannin kasashen larabawa da munafukan sarakunansu, amma kuma alokacin da musutane suka mike sai suka shiga gaba amatsayin sun e masu jagorancin irin wannan juyi da mutane suke domin kashin kansu.

Yanzu haka dai taron yana samun halartar mutane masana da suka hada da malaman jami'oi da na addini da kuma shugabannin kungiyi da 'yan siyas adaga kasashen larabawa da na musulmi daga ko'in acikin fadin duniya.

861858
captcha