IQNA

14:59 - September 17, 2011
Lambar Labari: 2188601
Bangaren siyasa, babbar manufar dukaknin juyi ita ce samun 'yanci da walwala da fita daga danniya da bautar mutane azzalumai masu danne hakkokin al'ummominsu, tare da kore hankoron yahudawan sahyuniya na baraka tsakanin al'umma.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalt daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya fadi a yau cewa, manufar dukaknin juyi ita ce samun 'yanci da walwala da fita daga danniya da bautar mutane azzalumai masu danne hakkokin al'ummominsu, tare da kore hankoron yahudawan sahyuniya na baraka tsakanin al'umma ta musulmi da kuma larabawan yankin baki daya.

A a cikin jawabinsa ya mayar da hankali kan muhimman abubuwan da ya kamata wadanda suka yi juyi a cikin kasashen larabawa su kula da su, domin kuwa kasashen yammacin turai sun sha alwashin ganin sun dankwafe yunkurinsu ta kowace fuska da dukkanin hanyoyi da za a iya bi.

Wannan bayanin nasa ya ci gaba da cewa, kasashe masu girman kai su ne wadanda suka hada kai da sauran azzaluman shugabannin kasashen larabawa da munafukan sarakunansu, amma kuma alokacin da musutane suka mike sai suka shiga gaba amatsayin sun e masu jagorancin irin wannan juyi da mutane suke domin kashin kansu kawai ab domin wani abu daban ba.

Taron dai yana samun halartar mutane masana da suka hada da malaman jami'oi da na addini da kuma shugabannin kungiyi da 'yan siyas adaga kasashen larabawa da na musulmi daga ko'in a cikin fadin duniya baki daya.

861859
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: