IQNA

Abubuwan Da Suke Faruwa A Yankin Za Su Kawo karshen Wahabiyanci

14:06 - September 18, 2011
Lambar Labari: 2189275
Bangaren kasa da kasa, sakamakon fadakar da al'ummomin yankin gabas ta tsakiya suka yi hakan zai sanya akidar wahabiyanci ta samu gagarumar matsalar da za ta iya rusa ta a tsakanin al'ummomin yankin.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na an bayyana cewa, sakamakon fadakar da al'ummomin yankin gabas ta tsakiya suka yi hakan zai sanya akidar wahabiyanci ta samu gagarumar matsalar da za ta iya rusa ta a tsakanin al'ummomin yankin da ma sauran kasashen musulmi da na larabawa baki daya.

Babban sakataren taron kasa da kasa kan farkawar Musulunci karo na faro da ake gudanarwa a kasar Iran Dr Ali Akbar Wulayati ya bayyana cewar yunkurin al'ummar kasashe da ya samo asali daga farkawar Musulunci yana jaddada adawar al'umma ce ga duk wani nau'in mamaya da babakere.
A jawabinsa a yayin bude zaman taron kasa da kasa kan farkawar Musulunci karo na farko da ake gudanawar a kasar Iran babban sakataren taron Dr Ali Akbar Wulayati ya jinjinawa mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu da duk wanda ya taka rawa a gwagwarmayar samar da wannan yunkuri na farkawar Musulunci a wannan zamani, domin yunkuri ne da ya yi sanadiyyar daukakar al'ummar musulmi.
Har ila yau Wulayati ya jaddada cewar wannan yunkuri ya zame wani babban abin alfahari ga al'ummar musulmi wanda tushensa ya samo asali daga kur'ani da sunna da irin rawar da al'umma ke takawa a fagen siyasa da zamantakewa. Kamar yadda yunkurin ya fadakar da al'umma kan neman wanzar da adalci a fagen siyasa da addini gami da adawa da duk wani nau'in zalunci da babakere.
861974








captcha