Bangaren kasa da kasa, shugaban yankin tsohuwar jamhuriyar Yeman ta kudu ya bayyana cewa juyin juya halin muslunci da ya wakana akasar Iran shi ne babban abin da ya haifar da juyi a cikin kasashen larabawa da ake gani a halin yanzu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, Ali Nase Mohammad shugaban yankin tsohuwar jamhuriyar Yeman ta kudu ya bayyana cewa juyin juya halin muslunci da ya wakana akasar Iran shi ne babban abin da ya haifar da juyi a cikin kasashen larabawa, wanda ake gani a halin yanzu suna neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulki da danniyar sarakuna da muggan shugabanni.
Ya ci gaba da cewa akwai bukatar a yi cikakken bayani kan abin da ake nufi da ta’addanci wanda ake cewa ana yaki da shi a duniya, domin kuwa akwai ta’addanci kuma akwai gwagwarmayar al’uummomi ta neman ‘yanci da fita daga kangi, wanda dukkanin abubuwan biyuan gwama su da suna ta’addanci.
Tsohon shugaban Yeman ta kudu ya ce juyin juya halin muslunci na Iran ya kawo babban sauyi a cikin dukaknin harkoki na yankin gabas ta tsakiya baki daya, kuma hakna zai ci gaba da yin gagarumin tasiri har zuwa lokacin da al’ummomin za su samu ‘yancinsu.
863037