IQNA

Juyin Juya Halin Musulunci Babban Abin Koyi Ne A Cikin Fadakar Musulmi

20:40 - September 19, 2011
Lambar Labari: 2190186
Bangaren kasa da kasa, shugaban majalisar koli ta msulunci a kasar Iraki ya bayyana juyin juya halin kasar Iran da cewa shi ne juyi da yafi dacewa masu bore a dukkanin kasashen musulmi da na larabawa su koyi da shi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-alam cewa, Sayyid Ammar Al-hakim shugaban majalisar koli ta msulunci a kasar Iraki ya bayyana juyin juya halin kasar Iran da cewa shi ne juyi da yafi dacewa masu bore a dukkanin kasashen musulmi da na larabawa su koyi da shi a cikin dukkanin yunkurinsu na juyi.
Sayyid Ammar Hakim Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa agaban taron fadakar musulmi na duniya da aka gudanar a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran, wanda ya samu halartar masana akalla dubu daya daga kasashen duniya tamanin, inda aka gabatar da wabai da bayar da shawarwari masu bore a kasashen musulmi da na larabawa na Afirka da yankin gabas ta tsakiya.
Ya kara da cewa hanyar ficewa daga mulkin danniya da zalunci na manyan kasashe masu girman kai ita ce mikewa domin neman ‘yanci na siyasa, kamar yadda Iran din ta bayar da kyakkyawan misali kan hakan a cikin lokatan da ta yi juyi, da kuma abin da ta aiwatar bayan juyin kamar yadda duniya ta sheda.
862980

captcha