Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta karyat rahotannin da wasu kafofin yada labarai na kasar suka watsa da ke cewa an kame wasu mambobin kungiyar da suke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila leken asiri.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadrawa na jaridar Ahram ta kasar Masar cewa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta karyat rahotannin da wasu kafofin yada labarai na kasar suka watsa da ke cewa an kame wasu mambobin kungiyar da suke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila leken asiri a cikin kasar ta Lebanon.
Bangaren yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar Hizbullah ya fitar da sanarwar da ke cewa wanann rahoto babu kamshin gaskiya acikinsa balantana madogara, wasu suka kirkire shi kawai domin su cimma wasu manufofinsu na siyasa, wanda hakan kuma ba zai yi wani tasiri ga kungiyar ba.
Wasu daga cikin jaridun kasashen larabawa da ba su boye tsananin gabarsu da kungiyar Hizbullah sun yi ta watsa wannan rahoto da nufin bat asunan kungiyar a tsaknain al’ummar kasar Lebanon, daga cikn jaridun da suka shiga gaba wajen watsa rahoto har da jaridar sharq Al-ausat ta gwamnatin Saudiyya.
866250