Bangaren kasa da kasa, dubabn palastinawa ne suka gudanar da zanga-zangar la’antar shugaban kasar Amurka Barack Obama, sakamakon furucin da ya fito daga bakinsa nakin amincewa a kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta a gaban babban taron majalisar dinkin duniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklatoo daga shafin sadarwa na aynar gizo na jaridar Al-bayan cewa, dubabn palastinawa ne suka gudanar da zanga-zangar la’antar shugaban kasar Amurka sakamakon furucin da ya fito daga bakinsa nakin amincewa a kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta a gaban babban taron majalisar dinkin duniya wanda yanzu hak ayake guda a birnin New York na kasar Amurka.
Shugaban palastinawa Mahmud Abbas tare da tawagarsa, sun mika takardar neman amincewa da kafa kasarsu mai cin gishin kanta ga babban sakataren majalisar dinkin duniya domin ya mika wannan takarda ga kwamitin tsaron majalisar domin kada kuri’a kan hakan domin amincewa ko rashin amincewa.
Kuma an mika wannan takarda kafin gabatar da jawabin shugaban palastinawa Mahmud Abbas a gaban wannan taro, wanda ga dukaknin alamu kasashen duniya sun nuna matukar gamsuwarsu da wannan mataki, inda suka yi rafsa masa tabi a lokacin da yake gabatar da jawabin nasa a gaban taron.
Tun kafin lokacin dai gwamnatin Amurka ta fito karara ta nuna rashin amincewarta da duk wani mataki da zai bayar da damar kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta, kuma ta sha alwashin yin fatali da wannan magana matukar dai aka gabatar da ita a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya wanda shi ne mataki na karshe.
866202