Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-ahram ta kasar Masar cewa an far agudanar da zaman taro na farko kan irfanin muslunci a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar tare da halartar wakilan kungiyoyi gami da malaman addinin muslunci da suka hada wakilin sakataren kungiyar hizbullah.
Wannan aya mai albarka tana zaburar da muminai zuwa ga kare hakkin dan adam, kare hakkokin mata da kanan yara da raunana, wadanda suka samu kansu karkashin mulkin danniya da zalunci, wadanda ba su da wani mai taimako baya ga Allah madaukakin sarki.
Wannan ya nuna a fili cewa daya daga cikin manufofin jihadi a muslunci shi ne kare ‘yan adam da ‘yantar da su daga zaluncin azzalumai, domin shi addnin muslunci a ko da yaushe yana girmama dan adam, yana kare hakkinsa, ba tare da banbanci a tsakanin mutane ba.
Aya mai alabarka tana kara bayani ne kan ayar da ta gabace ta, inda ta bayyana manufar jihadi a tafarkin Allah da cewa, muminai suna yin jihadi ne domin daukaka addinin Allah, yayin da wadanda suka bijire wa ubangiji suke yin yaki domin tabbatar da tafarkin shaidan da azzalumai.
866910