Bangaren kasa da kasa: al'umma a kasar Yamen Sun gudanar da zanga-zanga nuna adawarsu a fili karara a ranar hudu ga watan Mehr na shekara ta dubu biyu da dari uku da tis'in hijira shamsiya kan amincewa da Ali Abdallah Salih shugaban kasar dan kama karya ya yin a mika mulki bayan gudanar da zabe da cewa wannan wani sabon makirci ne da yaudara.
Kamfanin dillancin labaran Ikna da ke kula da watsa labaran harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musuluncin ta Iran ne ya watsa labarin cewa; al'umma a kasar Yamen Sun gudanar da zanga-zanga nuna adawarsu a fili karara a ranar hudu ga watan Mehr na shekara ta dubu biyu da dari uku da tis'in hijira shamsiya kan amincewa da Ali Abdallah Salih shugaban kasar dan kama karya ya yin a mika mulki bayan gudanar da zabe da cewa wannan wani sabon makirci ne da yaudara. A cikin wani jawabi ne day a gabatar ta hanyar talbijin din kasar ta yamen shugaban kasar ta Yamen dan kama karya day a share kwanaki masu tsawo yana sha magani a kasar Saudiya ya komo kasar ta Yamen tare da gabatar da jawabin da bai samu karbuwa ba daga al'ummar kasar ta Yamen masu fatar ganin an samu canji da sauyi a kasar da kuma ya sauka daga kan karagar mulkin day a share shekaru masu yawa a kai.
868427