IQNA

Kafofin Yada Labarai Sun Kasa Bayyana Hakikanin Ta’addancin Sarakunan Bahrain

20:33 - September 28, 2011
Lambar Labari: 2195260
Bangaren kasa da kasa, kafofin yada labarai na kasashen duniya sun kasa nakalto hakikanin abin da yake faruwa a kasar Bahrain an cin zarafin dan adam da keta hurumin addini wanda mahukuntan kasar suke aikatawa tun bayan fara zanga-zanga.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato wani rahoto daga shafin sadrawa na yanar gizo cewa, daya daga cikin fitattun ma’aikatan sadarwa na na kasar Kuwait Basil Al-dashti ya bayyana cewa kafofin yada labarai na kasashen duniya sun kasa nakalto hakikanin abin da yake faruwa a kasar Bahrain an cin zarafin dan adam da keta hurumin addini wanda mahukuntan kasar suke aikatawa tun bayan fara boren neman sauyi na siyasa a kasar Bahrain.
Ya ci gaba da cewa wajibi ne dukaknin musulmi da masu sauran lamirio aduniya su bayar da dukkanin gudunmawarsu wajen taimaka ma mutanen kasar Bahrain da suke fuskantar danniya da zalunci daga sarakunan kasar, da Amurka da Saudiiyya suke mara ma baya.
Dukkanin masu fafutuaka a sassa daban-daban na kasashen larabawa da ma wasu daga cikin kasashen yammacin turai suna ci gab ada yin Alla wadai da matakan rashin imani da fir’ananci da mahukuntan kasar Bahrain suke dauka kan fararen hula masu neman sauyi da hakkokinsu na ‘yan kasa.
868654

captcha