Bangaren kasa da kasa, kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun shafe duk wata alama ta musulunci ta hanyar yakin ruwan sanyi da suke yi da musulmi a wasu yankunan, a wasu kumata hanyar yaki da makami.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa fitaccen ma’aikacin jariidar nan na kasar Lebanon Sadiq Husaini ya bayyana cewa, babbar manufar kasashen yammacin turai ita ce hankoron ganin sun shafe duk wata alama ta musulunci ta hanyar yakin ruwan sanyi da suke yi da musulmi a wasu yankunan, a wasu kuma ta hanyar yaki da makami kamar yadda muke gani a kasashen larabawa da na musulmi da ke yankin gabas ta tsakiya.
A cikin abubuwan da aka ambata da suka gabata, ayoyi da dama sun yi mana ishara da cewa sharadin samun kyakyawan sakamako daga Allah shi ne imani da aiki na gari, wadannan ayoyi suna bayyana abin da ke cikin zuciyar mumini salihi na daga imani da mika wuya ga Allah, domin shi imani yana cikin zuciya ba abin da mutum ke fada da bakinsa ba kawai, domin kwa sau da yawa mutum zai iya bayyana imani a cikin ayyukansa amma cikin zuciyarsa ba mumini ba.
A lokacin da aikin mutum ya yi daidai da abin da ke cikin zuciyarsa na imani, a lokacin ne ya cika mumini, domin kuwa Allah madaukakin sarki yana kallon abin da ke cikin zukatan talikai ne.
868729