Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahotoo daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intikad ta kasar Lebanon cewa, wasu daga cikin yahudawan sahyuniya ‘yan share wuri zauna, sun baka wuta kan wani masallaci a yankin Jalil da ke arewacin palastinu da haramatacciyar kasar Isra’ila ta mamaye, wadanda sojojin haramtacciyar kasar Isa’ila take mara musu baya domin hana palastinawa mayar da martani kan wannan mummunan aiki.
Rahotaon ya tabbatar da cewa yahudawan da suka aiakta wannan danyen aiki mazauna wasu matsugunnan yahudawa ne da ke kusa wannan yanki na Jalil, inda suka kutso dauke da makamai, amma duk da hakan palastinawa ba su tsaya suna zura msu ido ba, alokacin da suke masallacin.
yahudawan sahyuniya sun yi hakan ne da nufin tsokanar palastinawa musulmi dasuke zaune ayankin, domin su shiga cikin rikici ta yadda za adauke hankulan al’ummomin duniya dangane da abin da ke faruwa na cin zarafin wannan al’umma da yahudawan sahyuniya suke yi tsawon shekaru, da kuma hana su kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta.
872472