IQNA

Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Madubi Ne Ga Farkawar Musulmi A Yankin

14:33 - October 05, 2011
Lambar Labari: 2199554
Bangaren kasa da kasa: juyin juya halin musulunci a Iran da Imam Khomeini ® ya jagoranta har ya cimma nasara wani babban madubi da abin koyi ga masu zanga-zangar neman kawo sauyi na musulunci a yankin gabas ta tsakiya kuma duk wani juyi na baya bayan nan na koyi ne da juyin juya halin musulunci na Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; juyin juya halin musulunci a Iran da Imam Khomeini ® ya jagoranta har ya cimma nasara wani babban madubi da abin koyi ga masu zanga-zangar neman kawo sauyi na musulunci a yankin gabas ta tsakiya kuma duk wani juyi na baya bayan nan na koyi ne da juyin juya halin musulunci na Iran.Hamid Alnajadi Abu Zahra malamin jami'a dan asalin kasar Iraki a jami'ar kasa da kasa ta London ya bayyana haka ne a lokacin wata tattaunawa ta musamman day a yi da kamfanin dillancin labarai na Ikna wanda ya jinjina wajibcin kungiyoyi da jam'iyun siyasa a yankin gabas ta tsakiya da su tashi tsaye don kare manufarsu mai muhimmanci da alfano .




872694
captcha