Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tahasar talabijin din Al-alam cewa, dubban mutanen kasar Saudiyya ne suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da halin da suke ciki a kasar na rashin adalci sakamakon tsarin mulukiya na kasar, wanda ya ginu kan danniya da fir’aunanci da mika wuya ga ‘yan mulkin malakka da yahudawan sahyuniya.
Yunkurin al'umma na farkawar musulmi da ya ke kan ganiyarsa a cikin kasashen yankin gabasa ta tsakiya,ya fara kwankwasa kofofin kasar Saudiyya. Kasar ta Saudiyya wacce ta kasance cikin sukuni na wani lokaci, a wannan lokacin ta fara jin tasirin yunkurin al'umma da ya ke faruwa a cikin kasashen larabawa. Taho mu gamar da aka yi a garin al-awamiyyha a gabacin kasar tsakanin mazaunansa da mafi yawancinsu mabiya mazhbar ahlul Bayti ne da kuma jami'an tsaro, yana a matsayin wata karaurawa ce ta hatsari ga mahukuntan kasar.
Rahotannin da su ke fitowa daga garin al'awamiyyah da ke yankin Qatif a gabacin Saudiyya sun ambaci yadda mutane su ka yi zanga-zangar lumana wacce ta sauye zuwa dauki ba dadi saboda shigar jami'an tsaro. Adadin mutane da su ka jikkata kuwa a wannan taho mu gamar sun kai 24, domin karkatar da hankulan mutane daga hakikanin abinda ya ke faruwa a kasa, ma'aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta danganta abinda ya ke faruwa da cewa kasashen waje ne su ka ingiza shi.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta musulunci mai cibiya a birnin London ta fitar da rahoto a ranar 4 ga watan nan na Oktoba da aciki ta bayyana cewa a cikin kasar Saudiyya ana tsare da fursunonin siyasa da adadinsu ya haura 30,000 kuma kungiyoyin kasa da kasa sun mance da su. Rahoton ya kuma ci gaba da cewa kama 'yan hamayyar siyasa a cikin Saudiyya wani abu ne da ya zama ruwan dare wanda kuma ya shafi kowane bangare na kasar ba tare da togiya ba.
Shugaban kungiyar kare hakkin bil'adam ta musuluncin, Ma'ud Shajarah ya fadi cewa manufar fitar da rahoton a wannan lokacin shi ne jawo hankalin al'ummar duniya da kuma kungiyoyin kasa da kasa dangane da halin da fursunonin siyasa su ke ciki a Saudiyya. Har ilayau rahoton ya bayyana gwamnatin zuriyar Ali'Sa'ud ta Saudiyya da cewa ta danniya ce da kuma kama-karya a fuskokin siyasa da al'adu da mazhaba. Mata basu da wani hakki ko kadan. Mabiya mazhabar ahlul-Bayti kuma a gabacin kasar ana mu'amala ne da su a matsayin 'yan kasa masu daraja ta biyu.
873778