IQNA

Hukumcin Zaman Gidan Yari har Kan Jagoran Jam'iyar Islami A Azarbaijan

15:48 - October 09, 2011
Lambar Labari: 2201679
Bangaren kasa da kasa; a wani mataki a fili na siyasa adawa da takurawa musulmi a kasar Azarbaijan wata kotu da aka kafa a garin Baku fadar mulkin kasar Azarbaijan ta hukumta Mausum Samda'uf jagoran jami'iyar Islami a kasar hukumcin zama a gidan yari na shekaru goma sha biyu.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a wani mataki a fili na siyasa adawa da takurawa musulmi a kasar Azarbaijan wata kotu da aka kafa a garin Baku fadar mulkin kasar Azarbaijan ta hukumta Mausum Samda'uf jagoran jami'iyar Islami a kasar hukumcin zama a gidan yari na shekaru goma sha biyu.Jam'iyar ta Islami a kasar ta Azarbaijan ana zarginta da kokarin kula makircin zagon kasa ga gwamnatin kasar zargin da yayan da mambobin jam'iyar ke yin watsi da shi da cewa wani salon e kawai na tsare mambobin jam'iyar da kuma yi masu bita da kulli.

875353


captcha