Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na min 20 cewa, babban malamin jami'ar Azhar ta kasar Masar ya yi kira zuwa ga gudanar da wani zaman tattaunawa tsakanin musulmi da kiristocin kasar, bayan barkewar rikicin da ya yi da sanadiyar mutuwar mutane da dama a cikin wannan mako, lamarin da ya bakanta ma da dama daga cikin malaman jami'ar.
Wani rahoton kuma yana nuni da cewa mambobin tsofuwar jam'iyar da ta yi milki a kasar Masar, wadda aka wargaza bayan boren al'ummar kasar a watan Janeru da febiryaru, sun bukaci magabatan kasar su basu damar shiga zabubbukan da za'a yi a kasar, wannan bukata ta zo a yayin da magabatan ke tattamnawa kan wani kudirin doka da zai iya hanasu shiga duk wata harakar siyasa a kasar har zuwa tsawan shekaru 10.
Sun bayyana wannan bukata ta su ne, bayan wani taro da mambobin jam'iyar ta PND da tsofon shugaban Hosni Mubarak ya jagoranta suka shirya a jiya Asabar a yankin sharquiya, inda suka shaida ma AFP cewa zasu shiga zabe. Tsofon Ministan Taimakon juna Ali El-Messeilhi ya ce wannan gagarumin boren na ranar 25 ga watan janeru, ba na kowa bane, ta al'ummar kasar masar ce baki daya a gaban dubunnan mutanen da suka taru.
Gurin wannan bore na jama'a shine na a kawo 'yanci, mutnci,demokarasiya, da shara'ar gaskiya tsakanin jama'a, ba a zabi wasu jam'iyoyi ba a ware wasu ba.
877086