IQNA

Majalisar Ministocin Kasar Masar Ta Gudanar Da Zama Kan Rikicin Da Ya Faru

20:22 - October 11, 2011
Lambar Labari: 2203260
Bangaren kasada kasa, majalisar ministocin kasar Masar ta gudanar da wani zama na musamman dangane da rikicin da ya faru a kasar cikin ‘yan kwanakin na wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla ashirin da shida.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi da ake bugawa a birnin Alkahira na kasar Masar cewa, a yau ne majalisar ministocin kasar Masar ta gudanar da wani zama na musamman dangane da rikicin da ya faru a kasar cikin ‘yan kwanakin na wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla ashirin da shida tsakanin jami’an tsaro da kuma mabiya addinin kirista na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin ministoci bakinsu ya zo daya kan a dauki matakan kusanto da fahimtar juna tsakanin dukaknin mabiya addinai a cikin masar, da nufin kauce ma duk wata mugama saboda rashin fahimta ta addini, kamar yadda suka jadadda wajabci kare hakkoki na dukkanin ‘yan kasar Masar.
Rahotannin sun habarta cewa, majalisar ministocin kasar Masar ta gudanar da wani zama na musamman dangane da rikicin da ya faru a kasar cikin ‘yan kwanakin na wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla ashirin da shida, kamar dai yadda majiyoyin jami’an tsaron kasar suka tabbatar.
877034

captcha