Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Ra’ad adnan tare da wasu daga cikin jami’an cibiyoyin kur’ani mai tsarki daga kasar Iraki, sun ziyarci babban ofishin kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna dake birnin Tehran domin ganin irin ayyukan da ake gudanarwa a wurin na kur’ani da kuma bunkasa harkokin al’adu na addinin muslunci, inda suka nuna matukar gamsuwarsu da jin dadinsu.
A wani bayanin kuma jagoran juyin juya halin na Musulunci ya kuma bayyana cewa: A kullum makiya suna cikin tunanin kulla sharri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne, amma Allah cikin ikonsa yana rusa duk wani makircin da suka kitsa. Jagoran ya kara da cewa: ko a cikin 'yan kwanakin nan kafofin watsa labaran da suke da alaka ta kud da kud da Yahudawan Sahayoniyya sun yi ta yayata zargi maras tushe da gwamnatin Amurka ta yi kan wasu Iraniyawa mazauna Amurka, a kokarin da Amurka ke yi na bata sunan kasar Iran tare da bayyana ta a matsayin kasar da ke kare ayyukan ta'addanci a duniya, amma wannan makirci babu wani tasirin da zai yi.
A cikin 'yan kwanakin nan ne dai gwamnatin Amurka ta hanyar kafofin watsa labaran da suke karkashin tasirin siyasarta suka dinga yada zargi maras tushe kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran na cewa wai tana shirya makarkashiyar aiwatar da kisan gilla kan jakadan Saudiyya da ke kasar Amurka, kuma har an kame wani ba'amerike dan asalin kasar Iran kan zargin, lamarin da ya bai wa gidan sarautar Ali-Sa'ud damar shelanta Iran a matsayin kasa mai hatsari a yankin gabas ta tsakiya.
Gwamnatin Amurka ta yi kokarin ganin ta hanyar wannan zargi maras tushe ta cimma bakar siyasarta kan kasar Iran, inda daga gabatar da zargi kan wasu mutane biyu kacal har ta fara batun daukan matakin kakaba ma kasar Iran takunkumi mafi muni da kokarin mai da ita saniyar ware a duniya. To sai dai wannan zargi na makirci ko a tsakanin jami'an Amurka bai samu karbuwa ba, inda masana harkar siyasa da na tsaro a cikin Amurka suka bayyana zargin a matsayin wasan yara da ba a zufafa tunani ba wajen gabatar.
880748