IQNA

Amsa Tambayoyin Maniyyata Zuwa Hajji Ta Hanyar Sadarwa Ta Internet

14:43 - October 20, 2011
Lambar Labari: 2208453
Bangaren kasa da kasa, an samar da wani shafi da ke amsa tambayoyin masu niyar tafiya zuwa aikin hajji da ma umra a kasar Saudiyya wanda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta dauki nauyin samarwa da sunan za ta taimaka ma maniyyantan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na naseej cewa an samar da wani shafi da ke amsa tambayoyin masu niyar tafiya zuwa aikin hajji da ma umra a kasar Saudiyya wanda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta dauki nauyin samarwa da sunan za ta taimaka masu gudanar da ayyukan haji da umra.
Mataimakin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya gabatar a gaban manema labarai, inda ya ce malamai da masana daga jami’o daban-daban na kasar saudiyya ne za su dauki nauyin kula da wannan shafi da kuma bayar da amsoshi ga masu tambaya.
Bayanin ya ce an samar da shafin da ke amsa tambayoyin masu niyar tafiya zuwa aikin hajji da ma umra a kasar Saudiyya wanda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta dauki nauyin samarwa, da nufin sawakae da dam adama daga cikin matsaloli da ake fuskantta alokacin aikin haji da umra, inda wasu ba su da masaniya kan abin da za su yi.
883030

captcha