IQNA

'Yan kabilar Gaddafi Ne Kawai Aka Yarje Ma Gudanar Da Sallar gawarsa

16:45 - October 25, 2011
Lambar Labari: 2211750
Bangaren kasa da kasa, babban malami mai bayar da fatawa a kasar Libya Sheikh Sadiq Garyani ya fitar da fatawar da ke haramta yi wa Gaddafi sallar gawa sai dai kawai ga danginsa ne a cewarsa ta halasta.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ahram ta kasar masar cewa, babban malami mai bayar da fatawa a kasar Libya Sheikh Sadiq Garyani ya fitar da fatawar da ke haramta yi wa Gaddafi sallar gawa sai dai kawai ga danginsa ne a cewarsa ta halasta kuma y ace hakan mahanga ce ta sharia ba ra'ayinsa ba.

Bayan kisan da aka yi wa shugaban kasar Libya dan kama-karya, Mu'ammar Gaddafi, an fara kokarin gano makomar Imam Musa Sadar. Gwamnatin Lebanon ta fara kokarin gano bakin zaren makomar malamin kuma shugaban majalisar koli ta musulunci a kasar.

A ranar lahadin da ta gabata ne wato 23 ga watan oktoba gwamnatin Lebanon ta aike da tawaga zuwa Libya wacce ta ke kunshe da alkalai domin ganawa da mahukuntan kasar akan makomar Imam Musa Sadar. Tawagar za ta sami cikakken bayanai da su ka shafi sace malamin da ya kafa kungiyar Amal da kuma kungiyar Talakawa marasa galihu a Lebanon. Haka nan kuma mutanen da su ka kasance a tare da shi da su ka hada da Sheik Muhammad Yakub da kuma wani dan jarida mai suna Abbas Badruddin.

A shekarar ne dai Mu'ammar Gaddafi ya gayyaci Imam Musa Sadar zuwa Libya domin halartar taron shekara-shekara na cin nasarar hawansa karagar mulki da ya ke kira juyin juya hali. Sai dai tun da ya shiga cikin kasar ta Libya bai fito daga cikinta ba.

Bugu da kari gwamnatin Lebanon za ta aike da wata tawaga daga ma'aikatun harkokin waje da kuma ta shari'a zuwa Libya saboda ta gana da dukkanin wadanda sunayensu su ke da alaka da batun Imam Sadar.

A gefe daya majalisar koli ta addinin musulunci a Lebanon ta dorawa gwamnatin rikon kwaryar Libya alhakin gano da bayyana makomar Imam Musa Sadar bayan gushewar shekaru 33 da shigarsa wannan kasa.

886150
captcha