IQNA

Babu Cikakkiyar Masaniya Kan Makomar Imam Musa Sadr A Libya

19:41 - November 03, 2011
Lambar Labari: 2216969
Bangaren kasa da kasa, tsohon alkalin babbar kotun sojin kasar Libya kuma babban mai bayar da shawara kan harkokin shari’a ga tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ya bayyana cewa sanin makomar Imam musa Sadr yana da matukar wahala.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin dil alalam cewa, tsohon alkalin babbar kotun sojin kasar Libya kuma babban mai bayar da shawara kan harkokin shari’a ga tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ya bayyana cewa sanin makomar Imam musa Sadr yana da matukar wahala a halin yanzu.
A bangare guda kuma shafin jaridar Telegraph ya habarta cewa, kasashen yammacin turai sun kasa boye damuwarsu kan yadda muslunci ke yin tasiri a boren da al’ummomin kasashen larabawa suke a cikin wannan lokaci, musamman idan aka yi lakari da kasashen da suka fara gudanar da zabuka kamar tunisia dag acikinsu.
Tun a farkon shekarar nan ne dai kasashen larabawa suka fara sheda bore mai tsanani wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar faduwar gwamnatoci uku, kumayake kan hanyar kawo karshen wasu gwamnatocin nakama karya a a cikin wasu kasashen larabawa. Kamar dai yadda ake shedawa.
Ko shakka bau kasashen yammacin turai sun kasa boye damuwarsu kan yadda muslunci ke yin tasiri a boren da al’ummomin kasashen larabawa suke a cikin wannan lokaci, musamman idan aka yi lakari da kasashen da suka fara gudanar da zabuka da cikin.
891813
captcha