IQNA

Kasawar Gwamnatoci Ya Bayyana na Biyan Bukatun Al'ummominsu

12:21 - November 14, 2011
Lambar Labari: 2222457
Bangaren siyasa: zabebben al'umma daga Kazwin yayi nuni da sauyin da ake samu a fadakarwar musulmi a yankin da cewa; a yau alhamdullahi al'ummomi sun tashi tsayin daga na kwatar lamari da makomarsu a hannu saboda yadda gwamnatocinsu suka nuna kasawarsu wajan biyan bukatun al'ummominsu.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ne ya watsa rahoton cewa; zabebben al'umma daga Kazwin yayi nuni da sauyin da ake samu a fadakarwar musulmi a yankin da cewa; a yau alhamdullahi al'ummomi sun tashi tsayin daga na kwatar lamari da makomarsu a hannu saboda yadda gwamnatocinsu suka nuna kasawarsu wajan biyan bukatun al'ummominsu.A wani zama ne da majalisar shawara ta jamhuriyar musulunci ta Iran ta gudanar a ranar ashirin da daya ga watan aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne yayi bayani kan yadda ake samin sauyi da canje canje a yau a harkokin siyasa da zamantakewar yankin da kuma yadda al'ummomin suka tashi na kwatar makomarsu a hannu ba tare da kasawa ba yayin da a bangaren hukumomi da gwamnatoci suka nuna kasawar.


897900
captcha