IQNA

21:31 - November 17, 2011
Lambar Labari: 2223870
Bangaren kasa da kasa, bababn sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah yana da mahanga kan addini daidai da yadda Imam Musa Sadr yake.

Wani labarin kuma na daban yana cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta sanar cewa ta samu wasika daga kungiyar hadin kan kasashen larabawa, da ke neman amincewar Syria domin aikewa da masu sanya ido daga kungiyar kan rikicin da ke faruwa a kasar.
Majiyar ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta sheda cewa za ta bayar da amsa ga kungiyar kasashen larabawan ba tare da wani bata lokaci ba. A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Qatar Hamad Bin Jasim ya fadi a wurin taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa a birnin Rabat na kasar Moroco cewa, sun baiwa Syria kwanaki uku ne da ta bayar da amsa kan wasikar, kuma suna shirin kakabawa Syria takunkumi na siyasa da harkokin tattalin arziki.
A ranar Asabar din da ta gabata ce kungiyar kasashen larabawan bisa matsin lambar Amurka da kasashen yammacin turai, ta sanar da dakatar da Syria daga cikin mambobinta, sakamakon rikicin da ke faruwa a kasar, wanda Syria ta zargi kasashen turai da ma wasu daga cikin kasashen larabawa da hannu kai tsaye wajen haddasa rikicin. Miliyoyin mutane ne a kasar Syria suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da kungiyar kasashen larabawan, tare da bayyana ta a matsayin 'yar koren Amurka da kasashen turai.
898074

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: