Bangaren kasa da kasa: a jiya juma'a ashirin da bakwai ga watan aban na shhekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya karkashin gayyatar kungiyar ikhwanul musulim a kasar ta Masar ,miliyoyin yan kasar sun gudanar da wata gagaramar zanga-zangar nuna adawarsu kan wasu ayoyin doka da aka tusa akundin tsarin mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa cewa: a jiya juma'a ashirin da bakwai ga watan aban na shhekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya karkashin gayyatar kungiyar ikhwanul musulim a kasar ta Masar ,miliyoyin yan kasar sun gudanar da wata gagaramar zanga-zangar nuna adawarsu kan wasu ayoyin doka da aka tusa akundin tsarin mulkin kasar.karkashin wannan gayyata ta kungiyar ikhwanul muslim a kasar ta Masar al'ummominin kasa a biranai daban daban sun gudanar da wannan zanga-zanga da amsa kiran na wannan kungiya domin nuna adawa da rashin amincewarsu kan yadda aka sanya wasu ayoyin doka a cikin daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar da ya bawa sojojin kasar wani karfin iko da hakan tamkar ba ta canja zane ba a kokarinsu na kawo canjin siyasa da mulkin kasar da kuma kifar da gwamnatin Husni Mubarakk a kasar ta Masar.
900112