Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-bayan cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro kan ayyukan cibiyoyin kur'ani a cikin nahiyar turai da kumayin nazari kan hanyoyin da za a kara bunkasa su da ayyukan nasu a cikin kasashensu.
A bangare guda kuma wani labarin na cewa, Shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Ali Larijani ya zargi kungiyar hadin kan kasashen larabawa da zama 'yar dakon manufofin Amurka, ya fadi haka ne a lokacinda ya ke gabatar da jawabi a kudu maso gabacin Iran ya ce, matakin da kungiyar kasashen larabawan ta dauka na jingine kasar Syria daga cikinta manufa ce ta Amurka
.
Shugaban na majalisar shawarar musulunci ta Iran ya ci gaba da cewa: " Me ya a lokacin da tankokin yakin gwamnatin Bahrain su ke kashe masu zanga-zangar lumana ba su dauki wani mataki ba, amma saboda biyawa Amurka bukata su ka dakatar da Syria. Kungiyar larabawan da Amurka su kwana da sanin cewa siyasarsu dangane da kasar Syria za ta ci kasa.
900143