Bangaren kasa da kasa, daruruwan mabiya addinin musulunci ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin New York an kasar Amurka domin nuna rashin amincewa da takurawar da jami’an tsaron kasar suke yi musu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na wnyc cewa, a yammacin jiya daruruwan mabiya addinin musulunci ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin New York an kasar Amurka domin nuna rashin amincewa da takurawar da jami’an tsaron kasar suke yi musu musamman ma a binin na New York.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wadanda suka gudanar da wannan zanga-zanga musulmi ne ‘yan asalin kasar Amurka da kuyma wasu wadanda suka je kasar kuma suke zaune a cikinta tsawon shekaru, babbar manufar hakan dai ita ce sanar da duniya halin da usulmi suke ciki a kasar Amurka da ke raya cewa tana kare hakkokin ‘yan adam da marassa rinjaye.
Wadannan daruruwan mabiya addinin musulunci ne suka gudanar da wata zanga-zanga a birnin New York an kasar Amurka domin nuna rashin amincewa da takurawar da jami’an tsaron kasar suke yi musu, kuma sun sha alwashin ci gaba da sanar da halin da suke ciki ga sauran mutanen duniya.
900803