Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo CPI ya habarta cewa, tawaga ta masu fafutuka daga sassa na kasashen duniya ta isa yankin zirin Gaza a yau domin ganewa idanunsu halin da al’ummar yankin suke ciki sakamakon killacewar da haamtacciyar kasar Isra’ila take yi wa yankin tun tsawon shekaru sama da shida da suka gabata.
Wani rahoton na daban kuma yana cewa Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a sakamakon fashewar wani shirgegen bam da aka dasa a gefen hanya a wani yanki da ke gabashin kasar Afghanistan a sanyin safiyar yau.
Rahotanni daga kasar sun ce bam din ya fashe ne a daidai lokacin da wata motar fasinja take wucewa a yankin, kuma daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara kanana 3. Kakakin gwamnan lardin Laghman inda lamarin ya faru Faizanullah Patan ya ce ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu akwai wasu mutane da dama da suka samu raunuka sakamakon fashewar wannan bam.
Ko a cikin makon da ya gabata wani jama'a da ke halartar aure a lardin na Laghman ya ci karo da wata nakiya da aka binne a karkashin kasa, kuma akalla mutane 7 ne suka rasa rayukansu a sakamakon wannan fashewar.
902573