IQNA

An Yanke Hukuncin Dauri A Gidan Kaso Kan Jagoran Masu Kiyayya Da Musulunci

22:37 - November 23, 2011
Lambar Labari: 2227976
Bangaren kasa da kasa, babbar kotun birnin Angers a kasar Faransa ta yanke hukunci daurin shekaru hudu a gidan kaso a kan jagoran kungiyar kyamar addinin muslunci da musulmi na kasar faransa bayan samunsa da laifin tunzura mutane domin kiyayya da wasu mutane babu gaira ba bu sabar.
Kamfanin dilalncin albaran iqna ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na islamophbie cewa, aynzu haka dai babbar kotun birnin Angers a kasar Faransa ta yanke hukunci daurin shekaru hudu a gidan kaso a kan jagoran kungiyar kyamar addinin muslunci da musulmi na kasar faransa bayan samunsa da laifin tunzura mutane domin kiyayya da wasu mutane babu gaira ba bu sabar, sai kawai domin suna bda banbacin ra’ayi na addini.
Wannan kungiya dai ta shahara matuka wajen kiyayya da musulmi a kasar Faransa, duk kuwa da cewa musulmi su ne na biyu a kasar faransa bayan kiristoci, amma kuma duk da hakan wannan bai sanya an karbi addinin musulunci a matsayin ba akasar faransa a hukumance, wanda wata kila hakan ne yake kara tunzura irin wadannan matasa wajen nuna kiyayya da adddini.
Babbar kotun birnin Angers a kasar Faransa ta yanke hukunci daurin shekaru hudu a gidan kaso a kan jagoran kungiyar kyamar addinin muslunci da musulmi na kasar faransa bayan samunsa da laifin tunzura mutane domin kiyayya da wasu mutane babu gaira ba bu sabar sai domin gaba da musulunci.
903055

captcha