Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi ta kasar Masar cewa, a cikin ‘yan lokutan nan haramtacciyar kasar Isra’ila ta nuna matukar damuwa dangane da makomar dangataka tsakaninta da kasar Masar a nan gaba matukar dai masu kishin islama suka karbi ragamatr harkokin mulki a kasar musamman ma abin da ya faru da ita a kwanakin baya.
A bangare guda kuma wasu rahotannin na cewa, gungun 'yan uwa musulmi a kasar Masar ya ce zai halarci tattaunawar da gwamnatin mulkin sojan kasar ta bukaci a yi a yau bayan share tsawon kwanaki uku ana artabu tsakanin jami'an tsaron kasar da kuma masu zanga-zangar neman sojojin kasar su gaggauta sauka daga kan karagar mulki.
Ita dai majalisar ta mulkin soja ta bukaci a gudanar da wata ganawa ne da wakilan kungiyoyi da kuma jam'iyyun siyasa na kasar dan samar da hanyoyin warware wannan sabon rikici da ya kunno kai ana sauran mako daya a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki wanda kuma shi ne zabe na farko da za'a gudanar a kasar tun bayan korar Husni Mubarak daga kan karagar mulki a cikin watan Afrilun da ya gabata.
A sakamakon tarzomar da ta barke a cikin kwanukan da suka gabata, akalla mutane 26 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu a kasar ta Masar, kuma wannan tarzoma ta baya bayan nan ta yi sanadiyyar gwamnatin rikon kwarya ta kasar gabatar wa shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar da marabus dinta duk da cewa shugaban ya ki amincewa da wannansafka.
904123