IQNA

Tabbatar Da Dukkanin Hakkokin ‘yan Shi’a A Lebanon Na Daga Manufogin Nasrallah

14:57 - November 24, 2011
Lambar Labari: 2228165
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin manufofin Sayyid Hassan Nasrallah ita ce dawo da dukkanin hakkokin mabiya mazhabar shi’a da aka haramta musu a kasar Lebanon a cikin shekarun da suka gabata tare da yin adalci a cikin dukkanin lamurra a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shfin sadrawa na yanar gizo cewa, daya daga cikin manufofin Sayyid Hassan Nasrallah ita ce dawo da dukkanin hakkokin mabiya mazhabar shi’a da aka haramta musu a kasar Lebanon a cikin shekarun da suka gabata tare da yin adalci a cikin dukkanin lamurra a kasar kamar yadda hakan ya zama manufar Imam Musa Sadr.
A bangare guda kuma kungiyar Hizbullah ta kasarLebanon ta maida martani akan rahoton Amurka dangane da yadda 'yan kungiyar leken asiri ta c.i.a su ka sha kasa,Mataimakin babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah, Sheikh Na'im Kasim ya fadi jaddada nasarar da Hizbullah ta samu na gano 'yan leken asirin c.i.a tare da rusa cibiyoyinsu, sannan kuma ya kara da cewa: " Kungiyar leken asirin ta c.i.a tana ci gaba da gudanar da ayukanta acikin Lebanon, kuma Hizbullah din za ta ci gaba da sa ido akanta."
Sheikh Na'im Kasim ya ce da akwai yaudara acikin yadda jami'an leken asirin Amurkan su ka bayyana cewa c.i.a ta dakatar da ayyukanta acikin lebanon saboda kashin da su ka sha, sai dai wannan ba zai aiki akan kungiyar ta Hizbullah ba."
Shi kuwa dan majalisar lebanon mai wakiltar Hizbullah Hassan Fadlallah ya bayyana karya lagon kungiyar leken asirin c.i.a a Lebanon din da cewa wata babbar nasara ce ga gwagwarmaya.
900375





captcha