Bangaren kasa da kasa, kwamitin malaman addinin muslunci na duniya ya yi kira da a kai dauki ga masallacin Qods da yahudawan sahyuniya ke shirin rusawa tare da sauran wurare masu tsarki da suke cikin birinin Akasa mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo cewa, babban kwamitin malaman addinin muslunci na duniya ya yi kira da a kai dauki ga masallacin Qods da yahudawan sahyuniya ke shirin rusawa tare da sauran wurare masu tsarki da suke cikin birinin Akasa mai alfarma da kuma mamaye kaddaroron al’ummar musulmi na palastinu da suke yankin.
A cikin wani bayani da ya fitar wanda jaridar Al-sharq ta kasar Qatar ta buga an bayyan acewa, wajibi ne kan dukaknin muslumi su mike domin ganin cewa an taka ma yahudawan sahyuniya birki kan abin da yake faruwa yanzu haka birnin Qods, domin kuwa yahudawan sun tashi haikan wajen ganin cewa rusa wannan masallaci mai albarka kowa ya rasa.
Yanzu haka dai kwamitin malaman addinin muslunci na duniya ya yi kira da a kai dauki ga masallacin Qods da yahudawan sahyuniya ke shirin rusawa tare da sauran wurare masu tsarki da suke cikin birinin Akasa mai alfarma, domin rashin yin wani katabus daga musulmi shi ne babban abin dake kara karfafa gwiwar yahudawan.
904815