Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na armennews cewa, gwamnatin kasar Armenia za ta dauki nauyin taron mabiya addinai na kasashen tsohuwar tarayyar Sovieta cikin mako mai zuwa da nufin kara karfafa laka tsakaninsu da kuma fahimtar juna da zaman lafiya wanda ak asan su da shi a tsawon tarihi.
Bayanin ya ci gaba da cewa zaman taron zai samu halartar jagororin addinan kiristanci musulunci da yahudanci, inda za su zauna su tattauna kan muhimman abubuwan da ya kamata su mayar da hankali kansu su da mabiyansu, musammn ma abubuwan da suka hada su, wadanda ba su sabanin fahimta a kansu.
Rahoton ya ce gwamnatin kasar Armenia za ta dauki nauyin taron mabiya addinai na kasashen tsohuwar tarayyar Sovieta cikin mako mai zuwa da nufin kara karfafa laka tsakaninsu da kuma fahimtar juna da zaman lafiya mai dorewa a tsakanunsu.
Zaman taron dai zai kwashe ‘yan kwanaki ana gudanar da shi, kuma daga bisani za a sanar da bayanin bayan taro kamar dai yadda masu shirya shi suka bayyana kan yadda zai gudana.
904796