Bangaren kasa da kasa:Kungiyoyin Hizbullahi da Amal a kasar Labanon a ranar hudu ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun fitar da wata sanarwar da ke cewa: sun hada guiwa a tsakaninsu inda suka bukatar gwamnatin Labanon da ta bukaci sanin makomar Imam Musa Sdre da kuma sauran mutanen da ke mara masa baya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa; Kungiyoyin Hizbullahi da Amal a kasar Labanon a ranar hudu ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun fitar da wata sanarwar da ke cewa: sun hada guiwa a tsakaninsu inda suka bukatar gwamnatin Labanon da ta bukaci sanin makomar Imam Musa Sdre da kuma sauran mutanen da ke mara masa baya.Kungiyoyin sun jaddada cewa bayan kifar da tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Kaddafi da kuma gwamnatinsa da kuma kasha shi babu abin da suke bukata kamar sake sanin makomar Imam Musa Sdare da wadanda suke tare da shi da tun lokacin da suka shiga kasar ta Libiya karkashin gayyatar Mua'ammar Kaddafin ba a sake jin duriyarsu ba.
905131