IQNA

Babban Malamin Azhar Ya Goyi Bayan Masu Zanga-Zanga A Dandalin Tahrir

16:03 - November 27, 2011
Lambar Labari: 2229946
Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami’ar Azhar da ke kasar Masar ya bayyana cikakken goyon bayansa ga matasan da suke gudanar da zanga-zanga a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira da nufin matsa lamba kan sojojin kasar da su mika mulki ga fararen hula.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na romandie cewa, Sheikh Ahamd Tayyib babban malamin jami’ar Azhar da ke kasar Masar ya bayyana cikakken goyon bayansa ga matasan da suke gudanar da zanga-zanga a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira da nufin matsa lamba kan sojojin kasar da su mika mulki ga fararen hula maimakon ci gaba da jan kasar kan mulkin majalisar soji.
Daya daga cikin malamn jami’ar da ya halarci dandalin Tahrir ya bayyana cewa, babban malamin yana goyon bayan abin da matasan suka bukata daga majalisar soji, kuma yana yin kira da a saurari abin da suke fada cikin koke-kokensu, domin kuwa abin da suke kira bai yi hannun riga da maslahr kasa ba.
Babban malamin jami’ar Azhar da ke kasar Masar ya bayyana cikakken goyon bayansa ga matasan da suke gudanar da zanga-zanga a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira da nufin matsa lamba kan sojojin kasar da su mika mulki ga fararen hula a karakshin mulki na demokradiyya.
Dubban daruruwan matasa ne ke ci gaba da yin zaman dirshan a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, domin jaddada matsayinsu na kin amincewa da mulkin soji. 905550
captcha