To kamar yadda dai aka sani muna cikin ranakun Muharram ne ranaku masu muhimmanci cikin tarihin Musulunci wadanda a cikinsu daya daga cikin taurarin Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) ya sadaukar da rayuwarsa da na iyalinsa da kuma mabiyansa wajen kare Musulunci da kuma tabbatar da asalin wanzuwansa. Hakan kuwa ta faru ne a ranar Ashura, wato ranar goma ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijirar Ma’aikin Allah (s.a.w.a) wato rana mai kamar ta gobe. Wannan tauraro da ya aikata wannan aiki shi ne Imam Husaini bn Ali (s.a.w.a). Don haka shirin na mu na yau zai yi dubi ne cikin rayuwarsa da kuma dubi cikin wannan batu na Ashura da irin matsayin da yake da shi wajen kare Musulunci.
To sai dai kafin mu je ga cikakken shirin muna isar da sakon juyayinmu ga Sahibul Asr Imam Zaman (ATFS) da dukkanin maraja’anmu masu girma da sauran al’ummar musulmi na duniya musamman mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) sannan kuma gare ku, ku masu saurarenmu saboda abin da ya faru a wadannan ranaku ga zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a) duk da cewa dai daga karshe dai jini ya yi nasara a kan takobi.
***************************
Masu saurare bisa la’akari da cewa a shirye-shriyen da muka gabatar muku a shekarun baya mun yi muku karin bayani kan abubuwan da suka faru musamman a ranar Ashura na irin zalunci da zubar da jinin zuriyar Annabi (s.a.w.a) da aka a wannan rana, sannan kuma cikin ‘yan kwanakin nan maganganun da ake yi kenan, watakila babu bukatar sai mun sake maimatawa. Don haka shirin na mu na yau zai yi kokarin dubi ne cikin dalilan da suka sanya Imam Husaini (a.s) ya yi wannan yunkuri nasa duk kuwa da ya yi amanna da cewa abin da ya faru da shi a ranar Ashura shi ne dai abin da zai faru da shi din matukar yayi wannan yunkuri. Har ila yau kuma za mu yi dubi cikin sakamakon wannan yunkuri da kuma abin da ya haifar wa Musulunci wanda idan da ba don yunkurawar Imam Husaini din ba watakila da a halin yanzu Musulunci bai zo gare mu ba. Wadannan bayanai dai su ne muke son yi wa mai saurare cikin dan wannan karamin lokaci da muke da shi.
To amma a matsayin share fage ba zai baci ba idan muka dan yi ishara ko da a gurguje ne kan wane ne Imam Husaini (a.s) don mu fahimci irin girman aikin da ya aikata sannan kuma mu fahimci irin girma da munin aikin da Umayyawa suka aikata a lokacin da suka kashe a ranar Ashura.
Da farko dai Imam Husaini (a.s) da yake wa Amirul Muminin Ali bn Abi Talib (a.s) da Fatima al-Zahra, ‘yar Manzon Allah (s.a.w.a), wato jika ne ga Manzon Allah (s.a.w.a) kuma daga cikin wadanda ya fi so a duk fadin duniyar nan. An haife shi ne a ranar 3 ga watan Sha’aban shekara ta hudu bayan hijira. Lokacin da aka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a) albishir da haihuwar Husaini (a.s.) nan take ya garzaya zuwa gidan Ali da Zahara (a.s), ya ce wa Asma’u bint Umais cewa: “Asama’u kawo min dana.” Sai ta kawo masa shi dauke a farin zane. Sai Manzo ya yi murna ya rungume shi, sannan ya kira salla a kunnensa na hagu, ya kuma yi ikama a na dama, sannan ya dora shi a cinyarsa sai aka ga yana kuka. Sai Asama’u ta tambaye shi cikin mamaki cewa: “Wa kakewa kuka?” Sai Manzo (s.a.w.a) yace: “ga wannan dan nan nawa.” Sai Asma’u ta ce: “Yanzun nan aka haife shi fa.” Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce: Asma’u, azzalumar kungiyar nan za ta kashe shi a bayana, kar Allah Ya hada su da ceto na.
Daga nan kuma bisa umurnin Allah, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya dubi Ali (a.s.) ya ce: “Ka sa masa suna Husaini. Wannan daya ne daga cikin falolin Imam Husaini (a.s) na cewa Allah Madaukakin Sarki ne ya sanya masa suna da kansa.
Matsayin Husaini (a.s.)
To yanzu kuma a gurguje bari mu yi dubi cikin matsayin Imam Husaini (a.s) kamar yadda muka ce daga nan kuma sai mu je ga asalin abin da muke son mu yi ishara da shi.
Imam Husaini (a.s) dai yana da babban matsayi. Bayan ayoyin Alkur’ani da suka ambaci matsayinsa cikin matsayin Ahlulbaiti (a.s.), irin su Ayar Tsarkakewa, Ayar Mubahala, Ayar Kauna da sauransu; hadisan Annabi ma sun kunshi nassosi masu yawa dake nuna girman matsayinsa da daukakar darajarsa. Daga cikin su akwai:
1-Abin da ya zo cikin Sahih al-Tirmizi cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Husaini daga gare ni yake, ni kuma daga gare shi nake.” Da cewa: “Allah Ya so wanda ya so Husaini.” Da cewa: “Husain (babban) jika ne daga cikin jikoki.” (mai son karin bayani yana iya duba littafin Fadha’ilul-Khamsah, juzu’i na 3, shafi na 263-263)
2-An riwaito daga Salman al-Farisi, ya ce: na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa:
Hasan da Husaini ‘ya’yana ne, wanda ya so su ya so ni, wanda kuma ya so ni Allah zai so shi, wanda kuwa Allah Ya so shi zai shigar da shi Aljanna. Kuma wanda ya fusata su ya fusata ni, wanda kuma ya fusata ni Allah zai yi fushi da shi, wanda kuwa Allah Ya yi fushi da shi zai shigar da shi wuta. (A’alam al-Warah, shafi na 219)
3-An riwaito daga Ali bin Husaini daga babansa, daga kakansa (a.s.), cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya kama hannun Hassan da Husaini (a.s.) sannan ya ce: Wanda ya so ni ya kuma so wadannan biyun da babansu da mahaifiyarsu, zai kasance tare da ni ranar kiyama (Sibt Ibin al-Jauzi, cikin Tazkiratu Khawas al-Ummah, babin da ya yi magana a kan ‘Son Manzon Allah ga Hasan da Husain’.
Wadannan kadan kenan daga cikin ruwayoyi masu yawan gaske da suke nuni da irin matsayin da Husain (a.s) ya ke da shi a wajen Allah Madaukakin Sarki. Daga ‘yan wadannan hadisi za mu iya fahimtar irin matsayin da kuma girman da yake da shi.
To za mu tsaya a nan dangane da abin da ya shafi falaloli da matsayinsa da ya ke da man ba a kansu ne muke son magana ba don kuwa a shirye-shryen da muka sha gabatar muku mun san hakan, don haka babu bukatar maimata su.
----------------------------
Dalilan Wannan Yunkuri Na Imam Husaini (a.s)
To kamar yadda muka ce za mu fi ba da muhimmancin kan dalilan da suka sanya Imam Husaini (a.s) yin wannan yunkuri na sa da kai ga abin da ya faru da shi a ranar Ashura don amsa tambayar da ake na cewa da wani dalili ne ya sanya Husain (a.s) zaban wannan tafarki na fito na fito da mahukuntan wancan lokacin.
A hakikanin gaskiya duk wanda ya bi tarihin rayuwar Husaini bin Ali (a.s.) zai fahimci cewa gudunmawarsa ga Musulunci ta fara ne da wuri. Domin ya taka muhimmiyar rawa a yunkurin Musulunci mai bunkasa a lokacin da bai fita daga matakin yaranta ba, a lokacin rayuwar mahaifinsa kenan da kuma a lokacin dan’uwansa Imam Hassan (a.s.). Duk da cewa bayan shahadar dan’uwansa Imam Hassan, aikinsa ya dauki wani sabon salo daidai da yanayin da ake ciki saboda kasancewar kowane Imami aikinsa na iyakantuwa ne daidai da dabi’ar yanayin zamantakewa, tunani da siyasa na lokacinsa.
Ko shakka babu Imam Husain (a.s.) ya kalubalanci wani mummunan shiri da kulli ne na Umayyawa na kokarin ganin bayan Musulunci da rayuwar Musulmi, musamman bayan yarjejeniyar sulhu da ta gudana tsakanin Imam Hassan (a.s.) da Mu’awiya. Wannan kulli na Umayyawa ya mayar da hankali ne a kan abubuwa kamar haka:
1-Yaduwar ta’addanci da kawar da duk wata kungiyar dake hamayya da mulkin Umayyawa, masamman mabiya Ali (a.s.).
Imam Bakir (a.s.) ya siffanta wancan yana yanayin yana cewa: “Ana kashe ‘yan Shi’armu a kowane gari. Aka yanke hannuwa da kafafu a bisa zato. (yanayin) Ya kasance duk wanda aka ji yana kaunar mu da zuwa wajen mu za a jefa shi a kurkuku ko a kwace dukiyarsa ko a rushe gidansa”.
Malaman tarihi dai na dukkan bangarorin musulmi sun yi karin haske kan hakan daga cikinsu kuwa akwai malamin tarihin nan Ibin Athir wanda a cikin littafinsa na al-Kamil Fit-Tarikh, juz’i na 3, shafi na 462 ya kawo yadda gwamnan Mu’awiya A Kufa Ziyad ya kashe dubban mutane yana mai cewa akwai wani lokacin da a dare guda kawai aka kashe mahaddata Alkur’ani 40.
2-Watsi da dukiya da nufin sayen lamirin mutane ciki kuwa da malamai da masu wa’azi da malaman hadisai.
3-Kuntatawa ta fuskar tattalin arziki da yin amfani da hanyar sanya mutane cikin yunwa, masamman a garuruwan da ba su mika wilayarsu gare su ba. Hakan kuwa a daidai lokacin da mahukunta ke wasa da dukiyar al’umma.
4-Rushe tushen ginin al’ummar Musulumi ta hanyar tayar da jin kabilanci da bangaranci, da rura wutar kabilanci a wajen larabawa a kan wadanda ba larabawa ba daga Musulmi.
5-Kashe Imam Hasan bin Ali (a.s.) duk da matsayin da ya ke da shi na halattaccen jagoran Musulmi.
6-Nadin da Mu’awuya ya yiwa dansa Yazidu a matsayin halifan musulmi a bayansa alhali kuwa Yazidu sananne ne wajen fajirci, shan giya da caca. Ko shakka babu yin hakan kuwa da nufin kawo karshen Musulunci ne da kuma komawa jahiliyya amma ta wani sabon salo.
Wannan Yazidun, kamar yadda tarihi ke tabbatarwa, lalacewa ta yi galaba a kansa, ta duk bangarorin tunaninsa da ayyukansa, ya kasance mashayin giya, mai bin ‘yan mata da wake-wake da duk sauran nau'i na sabon Ubangiji baya ga kisan kai wanda ya gada daga mahaifinsa.
Ibin Kathir cikin littafinsa na al-Bidayat wal-Nihayat, yayi karin haske kan irin wannan munanan halaye na Yazid.
Al-Masa’udi cikin littafinsa na cikin Murujul-Zahab, juzu’i na 3, shafi na 67 ya ce: Abin da Yazidu ya ke aikatawa na fasikanci ya yi tasiri a kan ma’aikatansa. A lokacin shi ne wake-wake suka bayyana a Makka da Madina, aka dinga aikata wasannin banza, mutane suka bayyana shan giya a fili.
Wadannan a bangaren abubuwan da suka faru kenan tun ma kafin nada Yazid a matsayin halifa da Mu’awiya ya yi. Bayan mutuwar Mu’awiya da kuma nada dansa Yazid a matsayin halifa abin da ya saba wa yarjejeniyar da ya cimma da Hasan (a.s) na cewa ba zai nada dansa a matsayin halifa a bayansa ba fa?
To da farko dai yana da kyau mu yi dubi cikin wadannan abubuwa:
Na farko dai: Yazidu dan Mu’awiyya ya dare karagar mulkin al’ummar musulmi, wanda a fili yake bai cancanci hakan ba face ma dai hakan wani babban hatsari ne ga makomar al’ummar. Yazid dai fasiki ne wanda bai sami komi kashin tarbiyya irin ta Musulunci ba, don kuwa ya girma ne a gidan da hasken rana ta shiriya ta Musulunci ba ta taba bulla a cikinsa ba, don haka ba abin mamaki ba ne irin har tarihi ya nakalto mana cewa Yazid dan giya ne, dan caca da dai sauran munanan ayyuka da suka saba wa dokoki da ka’idojin Musulunci. Hakan shi ne ya ba da dama ga duk wasu yin karen tsaye ga sakon Musulunci da dokokinsa, duk kuwa da cewa masu fatan alheri wa sakon Musuluncin – karkashin jagorancin Imam Husaini – sun yi amfani da wannan dama wajen kira da kuma jan hankulan mutane zuwa ga koyarwa ta hakika ta Musulunci. Don haka ne Imam Husaini (a.s) ya kasance duk wata dama da ya samu sai ya isar da wannan sako da kuma kiran mutane da su yi abin da ya dace kai hatta ma lokacin da dakarun Umayyawa suka kewaye shi a kasar Iraki sai da ya janyo hankalinsu ga hakan yana cewa:
“Ya ku mutane! Hakika Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Duk wanda ya ga ja’irin sarki, mai halalta abin da Allah Ya haramta, mai saba alkawarin Allah, mai yin karen tsaye ga sunnar Ma’aikin Allah (s.a.w.a), mai cutar da bayin Allah, to amma sai bai yi kokarin canza shi ba a aikace ko kuma da baki ba, to lalle ne Allah Zai shigar da shi makomarsa
Ta hanyar wannan huduba da ma wasunta, Imam Husaini (a.s) ya bayyanar da hakikanin yanayin gwamnatin Umayyawa, motsa zukatan al’umma da kuma kawar da kurar da ta rufe musu gaskiya.
Na biyu: Yanayin al’ummar wancan lokacin yanayi ne na zaman dirshan da babu wani kokari da ake yi wajen fuskantar mummunan yanayi na sabo da kauce wa hanya da ake ciki, hakan kuwa ya biyo bayan irin son jin dadi da kuma son kan da ke tattare da al’ummar ne, bugu da kari kan rashin ruhin tabbatar da abin da zai amfani al’umma gaba daya. Watakila hakan ne ma ya sanya wasu daga cikin manyan musulmi suka bukaci Imam Husaini da ya guje wa fuskantar gwamnatin Umayyawan. Saboda tsoron da ke cikin zuciyarsu. Hakan ne ma ya sanya mutanen Kufa nokewa da kin taimakon Husaini (a.s) duk kuwa da irin wasikun da suka aike masa na gayyatarsa zuwa wajensu. Watakila abin da zai tabbatar mana da irin wannan yanayi na mutanen Kufa, shi ne amsar da Farazdak ya bai wa Imam Husaini (a.s) lokacin da ya tambaye shi yanayin mutane a Kufan, sai ya ce masa: “Zukatansu suna tare da kai, amma takubbansu suna kanka (wato suna tare da Banu Umayya)”.
Hakika wadannan abubuwa suna daga cikin dalilan da suka sa aka kaddamar da wannan yunkuri mai albarka, don rayar da macaccen lamiri, da ba abin da yake ganin in ban da son duniya da kuma rayuwa. Don kuwa Imam Husain (a.s) ya riga da ya san cewa irin wannan yanayi mai ban haushi da al’ummar suke ciki a wancan lokacin ba shi da wata mafita ta shari’a ta kowani bangare, face ma dai shari’ar ce da kanta take kiran al’umma da su tsamar da kansu daga cikin duk wani yanayi da ba a gudanar da adalci da shiriya a cikinsa ba.
To bisa wannan fahimta da Imam Husaini (a.s) ya yi wa wannan sako na Musulunci – wanda shi ne asalin hakikanin addinin Allah a aikace – ya sa ya bayyanar da rashin amincewarsa a fili kan irin yadda al’amurra suke gudana a wancan lokaci.
Na uku: Don sanar da al’umma ma’anar Imamanci (shugabanci) na shari’a a mahangar Musulunci da kuma abin da ya kunsa: Hakika irin hatsarin da ke tattare da rawar da bakar siyasar Umayyawa ta taka a bangare ma’anonin Musulunci abu ne da ya saba wa ka’idoji (na Musulunci), don kuwa rawar ta faro ne daga wajen manyan jami’ai wadanda suka rike manyan hanyoyin wayar da kan al’umma. Babu shakka Imam Husaini (a.s) yana sane da hakan, don haka ne ma ya fara kokarin shiryar da kuma wayar da kan al’umma dangane da hatsarin da suke fuskanta daga mulkin Umayyawa a matsayinsa na mulkin da ya saba wa dokokin da koyarwa irin ta Musulunci. Hakan kuwa ya biyo bayan tsarin da Mu’awiyya ya fito da shi ne na gado da kuma kama karya yayin da ya tilasta wa mutane suka yi mubaya’a wa dansa Yazid.
Bisa la’akari da bukatocin Musulunci da kuma sharuddan da ya kafa kan shugaba, Imam Husaini (a.s) ya yi kokarin tabbatar da wannan lamari mai muhimmanci cikin zukatan al’umma ta hanyar jawaban da ya dinga yi a duk lokacin da ya sami irin wannan dama.
Na Hudu: Uzurin dan’Adam ba zai kasance abin karbuwa ba a mahanga shari’a ta Musulunci matukar ya gaza wajen aikata aikin da ya hau kansa. Don shi mutum a bisa shari’a ba halitta ce mai cin gashin kanta ba, face dai shi halitta ce da ke amsa bukatun sako na Musulunci, wajibi ne a kansa ya yi aiki da abubuwan da shari’ar ta tanadar masa, dole ne ya mika wuya da kuma sadaukarwa saboda ita. Hakika umurni da aikin alheri da kuma hani da mummuna da kuma jihadi don Allah da dai sauransu ba su kasance ba face hakikanin fassarar wannan ruhi da addinin Musulunci ya bai wa mabiyansa. Hakan kuwa ya yi daidai da ci gaban mutum a tafarkin koyi da sakon Ubangiji.
To yayin da Mu’awiya ya kuduri aniyar ayyana wannan da na sa Yazidu a matsayin halifa al’ummar musulmi (musamman kuma jagororinta wanda Imam Husaini (a.s) ya ke kan gabansu) ta sami kanta a wani sabon yanayi ne na tarihinta, wanda ya zama ba ta da zabi sai dayan biyu:
(A). Ko dai ta rungumi siyasar hamayya don tsige tushen barna da lalacewar da aka danfara mata; ko me han zai kallafa mata kuwa.
(B). Ko kuwa ta mika kai bori ya hau, wato ta amince da wannan yanayi kuma ta karbi wulakanci, kaskanci, tabewa da tsiraici.
Don haka Imam Husaini (a.s) a matsayinsa na dan Zakin Allah Ali kuma jikan Annabi Muhammadu (s.a.w.a) kana kuma dan sakon Musulunci sannan kuma bisa la’akari da irin taribiyyar da ya samu daga wajen kakansa Manzon Allah (s.a.w.a) da mahaifinsa Amirul Muminin (a.s) da mahaifiyarsa Fatima al-Zahra (a.s) da kuma Imam Hasan (a.s), babu makawa ba zai amince da irin wannan mummunan yanayi ba don haka ne ma yake cewa: "Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al'ummar kakana, Manzon Allah (s.a.w.a.). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana Aliyu bn Abi Talib”. A wani wajen kuma ya dada fito da hakan fili lokacin da gwamnan Madina Walid bn Utba bn Abi Sufyan ya bukace ya yi bai’a wa Yazid sai ya ce masa “Ya kai Sarki! Hakika mu ne mutanen gidan Annabci, mabubbugar sako, wadanda mala’iku sukan zo musu, da mu Allah Ya bude da mu kuma Ya rufe. Yazidu kuwa mutum ne fasiki, mashayin giya, mai kashe ran da aka haramta, mai bayyana fasikanci a fili. Don haka mutum kama ta ba zai taba yin bai'a wa mutum kamar Yazid ba.”
To saboda wadannan dalilai ne ya sa Imam Husaini (a.s) ya ki ya yi bai'a wa Yazid, kuma ma ya dau makami don yakansa, kamar yadda ya bayyana wa mabiyansa a duk inda ya yada zango don su fahimci matsayarsa ta siyasa da kuma irin halin da ake ciki.
A cikin wasikarsa ga mutanen Kufa, Imam Husaini (a.s) ya bayyana musu siffofin shugaba na kwarai, don ya wayar musu da kai da kuma bayyana musu wane ne ya cancanci ya zamanto shugaba. A cikin wasikar ya bayyana musu cewa:
"...Na rantse, shugaba shi ne wanda ya yi shari'a da Littafin Allah, wanda ya ke gudanar da gaskiya da kuma adalci, wanda kuma yake bayyanar da hakikanin addinin gaskiya, sannan kuma wanda ya ba da kansa don Allah".
Haka nan kuma ya rubuta wa manyan shuwagabanni Basrah; wato Malik bn Mas’ma’ al-Bukra, Al-Ahnaf bn Kais, al-Manzar bn al-Jarud, Mas’ud bn Amru, Kais bn Haitham da Amru bn Ubaid bn Mu’ammar wasika inda ya ke cewa:
"...Ina kiranku zuwa ga kiyaye Littafin Allah da Sunna ManzonSa (s) da kuma aiki da su. A halin yanzu an ajiye Sunnar Annabi (s) a gefe kana kuma an raya bidi'a. Matukar kuka riki wannan kalami nawa, to ni kuwa zan ja ku zuwa ga hanya madaidaiciya. Amincin Allah ya tabbata a gare ku”.
Hakika Imam Husaini (a.s) yana dubin gwamnati, siyasa, al'umma da kuma shugabanci ne a bisa mahanga ta Alkur'ani mai girma. To amma shi Yazid, sabanin haka, yana dubin wadannan al'amurra ne a bisa mahangar zalunci da babakere. Shugabanci, a wajen Imam Husaini (a.s), kamar wata mota ce wacce za a sanya mutane a kan tafarki shiriya da kuma isa zuwa ga hallarar Ubangiji, tafarki ne na sanya mutane a kan dokokin Ubangiji don su gina rayuwarsu a kan tafarkin gaskiya da kuma kyawawan dabi'u. A fahimtarsa, gwamnatin Musulunci tana karkashin kulawa ne na Musulunci da dokokinsa, wanda ta hakan ne za ta tsara nata dokoki da kuma ka'idoji. Haka nan kuma jami'an gwamnatin Musulunci, suna da alhakin kare manufofin al'umma da jin dadinsu, a takaice dai za su kasance abin tambaya a gaba ga Allah da kuma al'umma.
************************************
Daga wadannan bayanai za mu iya fahimtar dalilan da suka sanya Imam Husaini (a.s) zaban wannan tafarki na fito na fito da hukumar zalunci da lalata ta Yazid.
To da yake lokaci ya fara hararenmu bari mu karkare shirin na mu da sakamakon wannan yunkuri na Husain (a.s). Bayan mutuwar Mu’awiya akalar mulki ya fada hannun dansa Yazidu, sai ya hori gwamnoninsa da su karbi bai’a daga mutane, masamman daga Imam Husain (a.s.); wannan kuwa saboda irin masaniyar da gidan Umayyawa ke da shi na cewa shi – Husain - tsayayye ne da ba ya girgiza. Kamar yadda muka fadi dai Imam Husaini (a.s) ya ki ya yi masa mubaya’a don haka dai bayan matsin lamba Imam ya kuduri aniyar barin garin Madina tare da iyalansa inda ya nufi garin Makka. To daga can ma dai matsin lamba ya yi yawa, a bangare guda kuma ga wasikun mutanen Kufa nan na isowa ga Husain (a.s) suna kiransa da ya zo ya ‘yantar da su daga halin da suke ciki da kuma zama jagoransu.
Don sauke nauyin da ke kansa da kuma cimma wannan manufa ta haifar da sauyi Imam Husaini ya amince da wannan bukata ta su, don haka ya shirya barin Makka da kama hanyar Kufan. To sai dai daga baya sakamakon barazanar Umayyawa ya sanya mutanen Kufa juyawa da baya inda suka ha’inci Manzon Imam Husaini (a.s) wato Muslim bn Akil da kashe shi kana kuma suka shirya yakar Husaini (a.s).
Imam Husain (a.s) da mutanensa sun ci gaba da tafiya har rana ta biyu ga watan Muharram mai alfarma na shekarar hijira ta 61 inda Imam Husaini (a.s.) da mutanen gidansa da Sahabbansa suka isa sararin Karbala, wanda zai zama wani dauwamammen tsaiko ga ‘yantattu, kuma take ga masu ra’ayin juyi a tsawon tarihi da zamuna. A wannan waje ne dakarun Yazid karkashin jagorancin Umar bin Sa’ad suka tsare Husain da magoya bayansa.
Da farko dai sun bukaci Imam Husain da ya mika kai, amma ina Imam dai ya ci gaba da tsayawa a kan wannan matsayi nasa na cewa “Irina ba ya Mubaya’a ga irin Yazidu ”. Yana mai cewa: Ni ba na ganin mutuwa face dacewa, rayuwa da azzalumai kuwa (ba komai ba ce) sai kunci da tabewa”.
Don haka a daren goma ga watan Imam Husaini ya bukaci makiya din da su ba shi damar dare guda don amfani da shi wajen ganawa da Ubangiji da neman gafararsa don kuwa kamar yadda yace ba abin da ya fi so kamar salla da ganawa da Ubangiji. Haka kuwa ta faru, inda Imam Husain da magoya bayansa suka yi amfani da wannan dare wajen neman kusaci da Ubangiji.
Ko da gari ya waye dukkanin bangarorin biyu sun shirya fuskantar junansu, ko da yake a wannan lokacin ma sai da Imam Husaini ya sake kokarin kafa wa makiya din hujja da kuma tabbatar masa da matsayinsa da kuma wa suke so su yaka. Amma dai ina zukatansu sun riga da sun kekashe rashin imani sun cika su. Don babu abin da za a yi sai gwabzawa.
Don haka sai ya daga hannuwansa sama cikin kaskantar da kai da fuskantar Allah, yana cewa:
Ya Allah Kai ne amincina ga kowane bakin ciki, kuma Kai ne fatana a cikin kowane tsanani, kuma Kai ne amincina da tanajina cikin kowane al’amari da ya sauka gare ni. So nawa bakin ciki kan raunana zukata, dabaru su karanta a cikin shi, aboki ya gudu a cikin shi kuma makiyi ya daga kai; amma na mika shi gare Ka na kuma kai kara wajen Ka, ina mai wadatuwa da Kai daga waninKa; sai kuwa Ka yaye shi daga gare ni. Domin Kai ne majibincin kowace ni’ima kuma ma’abucin kowane kyakkywan abu kuma karshen kowace bukata.
Wannan shi ne farkon tashin hankali da abin takaici, wanda a sakamakon shi dan gidan Annabci kuma Imamin Musulmi Husaini bin Ali bin Abi Talib, jikan Manzon Allah (s.a.w.a) yayi shahada. Kamar yadda da yardar Allah a shirin mu na gobe za ku ji abin da ya faru din.
Inna lillahi Wa’inna Ilaihir-Raji’un.
“Kada ka yi zaton wadanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A’a, rayayyu ne su, a wurin Ubangijinsu. Ana ciyar da su”.
(Suratu Al’Imrana: 3:169)
Ana kirga kimar duk wani aiki na addini ko kuma na siyasa ne da irin tasiri da kuma sakamako na alherin da ya haifar da kuma canjin da ya kawo wajen gina rayuwar dan'Adam da kuma al'umma gaba daya. Akwai yiyuwar wannan tasiri da sakamako su banbanta saboda yanayi na siyasa da kuma lokaci kamar yadda kuma sukan iya kasance su dau wani lokaci mai tsawo ko kuma gajere kafin a ga tasirin. Akwai kuma yiyuwar tasiri da sakamakon su kasance ne a kan wani lamari na siyasa ko na zamantakewa ayyanannu ko kuma na wani lokaci kawai gwargwadon yanayi ko kuma zamanin da suka sami kansu, kamar yadda kuma sukan iya kasancewa fadaddu da suka mamaye ko ina ko kuma akasin hakan, da dai sauransu.
To don haka, wannan yunkuri na Imam Husain (a.s) ya kasance yunkuri ne mai girman gaske, ma'abucin kima da tasiri, mai fadaddiyar manufa, don kuwa manufarsa ba wai kawai ta takaita ne ga samun mulki da hukuma ba, duk kuwa da cewa dai Husaini (a.s) din ya yi amanna da cewa samun karfi irin na mulki wani wajibi ne na siyasa wajen kawo canji cikin al'umma, to amma dai manufarsa ba wai kawai ta takaita ga hakan ba ne. Imam Husain (a.s) ya kasance ma'abucin manufa mai girman gaske kana fadaddiya na kurkusa da na nesa, yana kallon mulki ne a bisa akidar da Mahaifinsa ya tabbatar:
"Ya Allah Ka san cewa abin da muke kokarin yi ba gasa ce don neman mulki ba, ko kuma neman mallakan dan abin da ya rage na abin duniya ba. Face dai abin da muke son yi shi ne dawo da alamun addnininKa da suka bace, mu raya dokokinKa da aka mance da su da kuma kare wadanda ake zalunta daga cikin bayinKa".
Hakika Imam Husain (a.s) yana son ne ya cimma wasu manufofi ta hanyar wannan yunkuri nasa, kamar:
1- Kawo sauyi cikin harkokin siyasa da kuma tsarin mulki da gudanarwa ta siyasa, bugu da kari kan mu'amala da al'umma gwagwardon dokoki da mizanin da Musulunci ya tabbatar da su.
2- Wayar da kan al'umma a bangaren siyasa da kuma mayar da su masu sa ido cikin lamurran gudanar da mulki don kada a kauce wa dokokin Musulunci.
3- Tabbatar da halalcin amfani da karfi a kan azzalumin shugaba.
4- Sake gina al'umma bisa ingantaciyyar tarbiyya.
5- Gyara kura-kuran da aka yi da kuma gudanar da shari'a da dokokinta.
6- Karya shamakin tsoro da fargaba da aka kafa wa al'umma da kuma motsa lamirin yunkuri da sadaukarwa tsakanin al'umma.
Mikewar Imam Husain (a.s) ke da wuya - duk da ya san da wuya wannan yunkuri na sa ya samu nasara ta soji face dai zai kasance ne wani mataki na farko na motsawar al'umma da kuma samun ruhin yunkuri - da sadaukarwar da suka yi sai ga shi wannan hukuma ta Umayyawa ta fara jijjiguwa da nufin faduwa kasa warwas. Don ta fara rasa alakar da take da shi da al'umma, duk kuwa da kokarin da ta yi na amfani da karfi da sauran nau'o'i na ta'addanci wajen kwantar da al'umma, amma al'ummomi sai nuna alamun bore su ke yi, sun fara jin shu'urin laifin kashe Imam Husain (a.s) da aka yi. Ko ina sai ruhin yunkuri da gwagwarmaya ta makamai don raunana da kuma kawar da gwamnatin Umayyawa ka ke gani, lamarin da daga karshe dai ya kawo faduwar gwamnatin Umayyawan warwas, hakan kuwa ya biyo bayan wannan yunkuri na Husaini (a.s) ne da kuma jininsa da na mabiyansa da suka zuba a kasar Karbala.
A matsayin misali, wannan yunkuri na Imam Husain (a.s) ya share fage wa Abdullah bn Zubair a Makka wajen yunkurin da kuma kawar da gwamnatin Umayyawa. Littattafan tarihi sun rubuto wasu daga cikin abubuwan da suka faru, wadanda suke nuni da tasiri da kuma sakamakon wannan yunkuri na Husain (a.s).
Al-Ya'akubi cikin Tarihinsa ya ce: 'Wani mutum ya ce: Wata rana na tafi wajen Abdul Malik bn Marwan, sai na gan shi tare da kan Mus'ab bn al-Zubair, sai na ce masa: 'Ya Amiral Muminina, hakika na ga wani abin mamaki a wannan guri', sai ya ce: 'Me ka gani'?, sai ya ce: 'Na ga kan Husaini bn Ali (a.s) a gaban Ubaidullah bn Ziyad, sannan kuma na ga kan Ubaidullah bn Ziyad a gaban al-Muktar bn Ubaidah, sannan kuma na ga kan Al-Mukhtar bn Ubaidah a gaban Mus'ab bn al-Zubair, to yanzu kuma ga shi na ga kan Mus'ab bn al-Zubair a gabanka' (Tarikh al-Ya'akubi, juzu'i na 2, shafi na 265).
Mutanen Madina sun kaddamar da yunkuri da bore a kan Yazid da gwamnansa Usman bn Muhammad bn Abi Sufyan, inda suka kore shi daga garin da dukkan Umayyawa. Wanda ya jagoranci wannan bore na mutanen Madina dai shi ne Abdullah bn Handhalah bn Abi Aamir. Sai dai daga baya sojojin mutanen Sham sun kawo hari garin Madinan inda suka keta huruminsa da zubar da jinin mutanensa. Al-Ya'akubi ya yin da yake siffanta wannan abin da ya faru a Madina da kuma yunkurin mutanen cewa ya ke yi:
"An kashe adadi mai yawa na mutanen (garin) da kuma keta hurumin Manzon Allah (s.a.w.a) da halalta wa sojojin Umayyawa garin ta yadda an samu budurwayen da suka haifi jariran da ba a san ubanninsu ba, don haka aka tilasta wa mutane mika mubaya'arsu ga Yazid bn Mu'awiyyah a matsayin bayi (Tarikh al-Ya'akubi, juzu'i na 2, shafi na 250).
Bayan wani lokaci dai an fara samun yunkuri da mayar da martanoni da suke kira zuwa ga daukan fansar jinin Husaini (a.s) ta yadda Husaini (a.s) ya kasance wani take na siyasa kana kuma karfi mai motsawa cikin tarihin gwagwarmaya da fada da zalunci. Lamarin dai ya soma ne da yunkuri Al-Tawwabun (Tubabbu) a garin Kufa karkashin jagorancin Sulaiman bn Sird al-Khuza'i da Musayyab bn Najbah al-Fazari, inda suka daga taken tuba da tunani kan gazawar da suka yi wajen taimakon Imam Husain (a.s) ta hanyar yakan Umayyawa da neman fansar jinin Husaini (a.s).
Daga nan kuma sai yunkurin al-Mukhtar bn Ubaidah al-Thakafi da Ibrahim bn Malik al-Ashtar a shekara ta 66 B.H., suna masu rera taken "Daukan Fansar Jinin Husaini". Sun sami nasarar ritsawa da wadanda suka kashe Husaini (a.s) inda suka kashe Ubaidullah bn Ziyad, Husayn bn Numayr da Umar bn Sa'ad.
Wannan ruhi na gwagwarmaya da yunkuri dai ya ci gaba har lokacin da gwamnatin Umayyawa ta fadi a hannun masu yunkurin Abbasiyawa, wadanda a zahiri suke kira zuwa ga mayar da al'amurra ga Ahlulbaitin Manzo (s.a.w.a).
Ta haka ne dai jinin Imam Husain (a.s) ya kunna wutan yunkuri da bore wa hukumar Umayyawa da kawo karshen kasantuwansu a fagen siyasa har aka kawo karshensu dai gaba daya. Babu shakka Husaini (a.s) zai ci gaba da kasancewa taken ma'abuta yunkuri kana kuma fitila ga ma'abuta 'yanci sannan makaranta ta gwagwar-maya da kuma 'yanto al'umma.
Aminci ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi da ranar da ya yi shahada da kuma ranar da za a tashe shi rayayye.
"Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai"